A bayyana abin da za a iya wa Sakkwatawa da tallafin Gwamnatin Tarayya – Gumburawa
Tsohon dan Majalisar Wakilai daga mazabar Kware da Wamakko Alhaji Sa’idu Muhammad Gumburawa ya bukaci Gwamnan Jihar Sakawato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana wa Sakkwatawa abin da zai musu da kudin da Gwamnatin Tarayya ta bayar don amfanin jama’a da saukaka al’amuran a jiha.Alhaji Sa’idu Gumburawa ya ce akwai bukatar Gwamna Aminu Tambuwal ya […]
Tsohon dan Majalisar Wakilai daga mazabar Kware da Wamakko Alhaji Sa’idu Muhammad Gumburawa ya bukaci Gwamnan Jihar Sakawato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana wa Sakkwatawa abin da zai musu da kudin da Gwamnatin Tarayya ta bayar don amfanin jama’a da saukaka al’amuran a jiha.
Alhaji Sa’idu Gumburawa ya ce akwai bukatar Gwamna Aminu Tambuwal ya yi nazari da neman shawara don sanin matsalar da Sakkwatawa suke ciki kafin zuwan wannan kudi da
aka bayar na tallafi, “Muna jiransa ya yi mana bayanin tsare-tsaren gwamnatinsa da kudin da ake turo masa,” inji shi.
Ya kara da cewa “Jihar Sakkwato a kowace shekara tana daukar kofin jiha mafi talauci a Najeriya saboda kudin da ake kawowa ba a san yadda ake yi da su ba, ko kwangila ba ’yan jihar ake baiwa ba, ina yi wa Tambuwal fatan alheri ya samu nasarar fitar da Sakkwatawa daga halin da muke ciki.”
Ya ce su ’yan adawa a Jihar Sakkwato kamar ba ’yan jiha ba ne, ba a komai da su duk yadda suka kai da cancanta, balle su nuna ra’ayinsu, “Ka dubi yadda ake rike wa wasu albashi babu takardar gargadi ko sallama an danne musu hakki kuma babu abin da za a yi, a Jihar Sakkwato ce kawai ake haka don ka yi jam’iyar da ba ta samu nasara ba. Misali a karamar Hukumar Wamakko mutum 35 nake da labarin an yi musu haka ba tare da an nuna musu takardar laifi ba,” inji shi.
Ya ce suna kuma bukatar sanin bayanan abubuwan da Gwamna Tambuwal ya gada daga gwamnatin Aliyu Magatakarda Wamakko da sanin bashin da ya gada da sauran abubuwan da ya kamata su sani.
Gumburawa ya ce jam’iyyarsu ta PDP a jihar tana da matsaloli saboda ba ta da jagora da zai iya hada kan mutane wuri daya don cimma manufar siyasa ta jama’a ba ta mutum daya ba.
Ya ce bai kamata wani a jam’iyyar ya ce ra’ayinsa kawai za a yi ba, inda ya yi zargin an sanya son kai da son rai kuma shi ne matsalar da PDP ta samu kanta a jihar.