A binciki jami’an tsaro kan hare-haren da ake kaiwa a Najeriya – Nalele
Mataimakin shugaban kungiyar ’yan kasuwa ta karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato Alhaji Habibu Nalele ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya kan ta binciki jami’an tsaro dangane da hare-haren da ake kaiwa a ’yan kwanakin nan a jihohin Barno da Yobe da Adamawa. Alhaji Habibu Nalele ya yi wannan kiran ne a lokacin […]

Mataimakin shugaban kungiyar ’yan kasuwa ta karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato Alhaji Habibu Nalele ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya kan ta binciki jami’an tsaro dangane da hare-haren da ake kaiwa a ’yan kwanakin nan a jihohin Barno da Yobe da Adamawa.
Alhaji Habibu Nalele ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos inda ya ce daukar wannan mataki ya zama wajibi idan aka yi la’akari da yadda maharan ke zuwa su kawo hari su kashe mutane su tafi ba tare da an kama kowa ba.
Alhaji Habibu Nalele ya ce Najeriya ta sha tura dakarunta zuwa kasashen duniya don kwantar da rikice-rikice kuma sun samu nasarori masu yawa. “Amma abin ya gagara a nan Najeriya, wannan abin dubawa ne kuma abin tunani ne,” inji shi.
Ya ce abin da mamaki muna da jami’an tsaro na farin kaya da na SSS wadanda za su iya bincike kan lamarin don gano wadanda suke taimaka wa maharan da wuraren da suke samo makaman da suke amfani da su.
Alhaji Nalele ya ce idan gwamnati ba ta dakatar da rikicin ba, zai iya durkusar da kasar nan. “Kuma ina kira ga al’ummar Arewa Musulmi da Kirista, sarakuna da malamai da fastoci a koma ga Allah a yi ta addu’a Allah Ya kawo karshen wannan rikici.