A binciki tashin hankalin Zariya

Aminiya tana kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi kwakkwaran bincike a kan abin da ya faru a Zariya.  Kuma ya kamata Hukumar Kare ’Yancin dan Adam ita ma ta shiga cikin batun don ganin an yi binciken da ya dace.  Sannan kada binciken ya takaita a kan abin da ya faru a Zariya kadai, ya […]

A binciki tashin hankalin Zariya
A binciki tashin hankalin Zariya

Aminiya tana kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi kwakkwaran bincike a kan abin da ya faru a Zariya.  Kuma ya kamata Hukumar Kare ’Yancin dan Adam ita ma ta shiga cikin batun don ganin an yi binciken da ya dace.  Sannan kada binciken ya takaita a kan abin da ya faru a Zariya kadai, ya hada da neman amsar me ya sa sojoji suka yi amfani da bindiga wajen kashe mabiya Shi’a da hakan ta sa aka hallaka fararen hular da ba su ji ba, ba su kuma gani ba?  Sannan a yi binciken yadda aka hallaka ’yan Shi’a masu yawa a wata hatsaniya da ta faru a farkon shekarar nan a tsakanin kungiyar da jami’an tsaro.
Idan aka kyale batun ya ci gaba aukuwa ba tare da an yi wa tufkar hanci ba, to akwai yiwuwar ya shafi wani ko wasu a nan gaba ba ’yan Shi’a kadai ba. Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa don ganin an yi adalci ga duk wanda aka zalunta musamman wadanda aka kashe da kuma wadanda aka lalata wa dukiya. Sannan Majalisar Dokoki ta kasa ta sanya ido a binciken don ganin an yi adalci ga kowa.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno