A binciki tashin hankalin Zariya(9)
Tashe-tashen hankulan da suka faru a Zariya a ranakun Asabar da Lahadin da suka gabata abin takaici ne musamman yadda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa. Tashin hankalin ya fara ne kamar da wasa a tsakanin mabiya akidar Shi’a da jami’an sojojin da ke yi wa Shugaban Sojojin Najeriya Laftana Janar Tukur Yusuf […]
Tashe-tashen hankulan da suka faru a Zariya a ranakun Asabar da Lahadin da suka gabata abin takaici ne musamman yadda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa. Tashin hankalin ya fara ne kamar da wasa a tsakanin mabiya akidar Shi’a da jami’an sojojin da ke yi wa Shugaban Sojojin Najeriya Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai rakiya. Mabiya akidar Shi’a sun tare hanya ne a lokacin da jami’an sojojin suke kokarin wucewa amma mabiya Shi’ar suka kekasa kasa suka hana su wucewa. An nuna sai da manyan jami’an sojin suka sauka daga motocinsu don lallashin mabiya Shi’ar na su yi hakuri su ba su hanya don su wuce amma suka kekasa kasa suka ki, daga karshe dai ba zato ba tsammani sai sojojin suka bude musu wuta inda aka yi asarar rayuka da dama. Rahotanni sun nuna ’yan Shi’ar sun tare hanyar ce a lokacin da suke bikin Mauludi da suke yi wa lakabi da Hussainiyya Bakiyatullah inda suka tare hanyar da ta hada PZ da Samaru kuma suka hana motoci da mutane da ke amfani da hanyar sakat. Rahoton ya nuna akalla mutum uku aka kashe a lokacin hatsaniyar.
Kakakin Sojin Najeriya, Kanar Sani Kuka-sheka Usman daga baya ya fitar da wata sanarwar da ta nuna sojojin sun kai wa ’yan Shi’ar hari ne a kokarin kare kansu a yunkurin da suka yi na hallaka shugabansu Tukur Buratai. Ya ce masu zanga-zangar sun yi amfani da manyan duwatsu wajen rufe hanya kuma ba zato ba tsammani sai suka fara jifansu da duwatsu, inda suka mayar musu da martani a kokarin kare kansu. Hasalima ya ce yin haka tamkar yunkurin hallaka shugaban sojoji ne da ’yan kungiyar suka yi.
A ranar Asabar da yamma kuma sai mabiya Shi’a suka fitar da sanarwa inda suka musanta zargin da sojojin suka yi musu cewa sun kai musu hari. Kakakin ’yan Shi’ar, Ibrahim Usman ya ce ba su yi yunkurin hallaka shugaban sojoji Buratai ba, amma sun toshe manyan tituna ne don su tsaurara matakan tsaro saboda gudun kada abin da ya faru da su a Kano a kwanakin baya ya sake faruwa a lokacin da wasu suka kai musu harin kunar bakin wake da ya yi sanadiyyar hallaka mabiyansu da dama.
A ranar Asabar da daddare sai abin ya sake kazancewa bayan sojoji sun sake kai hare-hare a wurare uku da mabiya Shi’a suke taruwa. Da farko sun kai hari gidan shugabansu Sheikh Ibrahim Zakzaky da ke Gyallesu sannan suka kai wani hari a sansanin da suke taruwa da ake kira Hussainiyya Barkiyatullah da ke Unguwar Turawa (GRA) sannan da harin da suka kai a wani wurin taron ’yan Shi’ar da ke wajen birnin Zazzau.
Jama’a da dama ba su yi barci ba a ranar Asabar da dare zuwa wayewar garin Lahadin, inda suka ce an kwashe daukacin daren suna jin harbe-harbe.
Bayan al’amurra sun lafa ne sai aka samu labarin mutuwar mutane da dama. Rahotanni sun nuna an kashe danZakzaky mai suna Sayid Ali a harin da Mataimakin Shugaban ’yan Shi’ar, Sheikh Mahmud Muhammad Turi da likita mai kula da lafiyarsu Dokta Mustapha da kuma Kakakin kungiyar Ibrahim Usman. Duk da yake kawo yanzu ba a bayar da adadin wadanda suka rasa rayuka a harin ba, amma mazauna birnin sun tabbatar an kwashi gawarwakin da ba a san yawansu ba a ranar Lahadi da safe.
Ga dukkan alamu, sojojin sun dauki wannan mataki ne saboda harzuka su da ’yan Shi’ar suka yi ba. Gaskiyar magana ita ce mahukunta da mazauna birnin Zariya da ma na wasu sassan kasar nan ba kasafai suke jin dadin yadda kungiyar Shi’a take gudanar da harkokinta ba a duk lokacin da suke gudanar da taro musamman wajen rufe hanyoyi da wasu muhimman wurare. Mazauna wurin da ’yan Shi’a suke gudanar da tarurruka sukan zama tamkar bayi inda ba sa samun sukuni har sai sun gama taron. Hakan ya sa wasu ke tunanin kungiyar tana yin abin da ta ga dama wajen karya doka ba tare da hukuma ta tsawata musu ko neman hana su ba, watakila saboda tsoro ko don neman a zauna lafiya.
A da ’yan Shi’a suna gudanar da taro ne sau daya a shekara. Suna yin taro ne a ranar kudus inda suke nuna goyon bayansu ga Falasdinawa saboda mamayewar da Isra’ila ta yi musu. Daga baya ne abin ya canja inda suke yin tarurruka a mafi yawan lokuta. Hakan ya sa jama’a da dama abin ya gundure su don ba a son ransu ake yin irin wadannan tarurruka ba. Haka kuma yadda kungiyar Shi’a ke amfani da hanyoyin sadarwa na Intanet wajen watsa tarurrukan da suke gudanarwa a sassan kasar nan da yadda suke nuna yadda suke samun horo (fareti) duk da yake ba kasafai suke amfani da makamai ba, shi ma abin takaici ne.Yin haka ya nuna tamkar wata hukuma ce ta daban duk da suna karkashin gwamnati ne. Bai dace hukuma ta zuba ido ta bari irin haka na faruwa ba.
Amma ya dace jami’an tsaro su yi amfani da hanyar lalama musamman a wannan lokaci na mulkin dimokuradiyya wajen lallashin kungiyar ’yan Shi’a don ganin ta daina yin fito-na-fito da dokokin kasa. Ya kamata a rika kai wadanda suka karya dokar kasa kotu ne maimakon amfani da bindiga wajen yin kisa.
Abin da ya faru a karshen makon jiya tamkar irin wanda ya faru ne a watan Yulin shekarar 2009 a lokacin da aka kama shugaban ’yan Boko