A binciki wannan zubar da jinin
Rahotannin da suka fito daga Zariya a ranar Juma’ar makon jiya sun bayyana an yi bata-kashi tsakanin sojoji da ’yan Shi’a, inda aka bayyana mutuwar mutum 35. Al’amarin ya faru ne a lokacin da ’yan Shi’a ke gudanar da muzaharar shekara-shekara da suka saba kan yadda Isra’ila ta kori Falasdinawa; ranar da suka yi mata […]
Rahotannin da suka fito daga Zariya a ranar Juma’ar makon jiya sun bayyana an yi bata-kashi tsakanin sojoji da ’yan Shi’a, inda aka bayyana mutuwar mutum 35. Al’amarin ya faru ne a lokacin da ’yan Shi’a ke gudanar da muzaharar shekara-shekara da suka saba kan yadda Isra’ila ta kori Falasdinawa; ranar da suka yi mata lakabi da ‘Ranar kudus.’
An fara gudanar da muzaharar shekara-shekarar ce a Iran a 1980, wato a lokacin da Shugaban Addini na Iran Ayatollah Khomeini ya umarci ’yan Shi’a da yi muzaharar sakamakon musgunawar da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa.
An fara wannan muzaharar a Najeriya shekara 30 da suka gabata, don haka ba wannan ne karo na farko da ’yan Shi’a suka fara gudanar da muzahara a kasar nan ba.
Rahotannin daga Zariya hedikwatar ’yan Shi’a a Najeriya kuma garin da shugaban ’yan Shi’a a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky yake zaune, sun nuna al’amarin ya faru ne dalilin hana sojoji da wucewa da ’yan Shi’a suka yi yayin da suke muzahara a kan titunan garin, jami’an tsaro ba su ce haka ba, amma sun yi magana mai kama da haka, kamar yadda mai magana da yawun sojojin Najeriya Birgediya-Janar Olajide Laleye ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa, “Ba sojoji ne suka nemi tsokana har suka fara harbi ba, sun fara harbi ne don su kare kansu bayan ’yan Shi’a sun bude musu wuta,” amma ’yan Shi’a sun ce wata makarkashiya aka shirya don kawai a yi musu kisan gilla. A yanzu an samu sabani kan yawan mutanen da suka rasa rayukansu.
Wannan al’amari ya kara dakusar da harkar kasuwanci da kuma haba-haba da walwalar jama’a a Zariya, sakamakon dar-dar da jama’a suke yi dalilin rikicin Boko Haram da ya sanya ba a yi hawan Sallah ba.
Mai magana da yawun sojojin Najeriya ya ce ’yan Shi’a tara ne suka mutu, su kuma ’yan Shi’a sun ce an kashe musu mutum 35.
Mun dade muna lura da yadda jami’an tsaro ke daukar al’amarin addini a kasar nan, don haka muna kira ga muhukunta su yi adalci wajen bincike kan al’amarin da ya faru.
Ba wai fata muke yi ba, amma ya kamata a fahimci irin haka ne ta faru har muka samu kanmu cikin rikicin Boko Haram da ya addabi kasar nan. A lokacin jami’an tsaro ba su yi abin da ya dace kan matsalar musamman a farko-farkonta ba, musamman irin yadda aka yi wa shugaban ’yan Boko Haram Mohammed Yusuf kisan gilla, al’amarin ya sanya Abubakar Shekau daukar matakin ba sani ba sabo a kan kowa.
Wannan jarida ta yaba irin kokarin da Sheikh Zakzaky ya yi wajen kwantar da hankalin jama’arsa duk da cewa an kashe masa ’ya’ya uku. “Ina rokon mabiyana su yi hakuri, su kwantar da hankalinsu. Bayan kisan gillar da aka yi mana, za mu ga wane mataki ya kamata mu dauka,” inji shi.
Tabbas yana da kyau mu kawo abin da Sheikh Zakzaky ya bayyana wa ’yan jarida a Zariya a ranar Asabar. “Lokacin da jami’an tsaro suka far mana, jama’a da dama sun mutu da yawa sun samu raunika, a cikinsu akwai kananan yara da mata. A lokacin da ake harbe-harben ne aka harbe dana Mahmud wanda dalibi ne a Jami’ar Al-Mustapha International Unibersity da ke Beirut a Lebanon. Ya zo hutu ne a farkon Ramadan. An kuma harbe shi a ciki. An kawo shi wurina cikin jini, sai suka yi yunkurin kai shi asibiti, amma babu dama saboda sojoji sun tsare hanya. Haka ya rika zubar da jini a karshe ya mutu a kan hanyar zuwa asibiti,” inji shi.
“A cikin wadanda aka kama akwai ’ya’yana Ahmad da Hameed da kuma Ali. Sojojin sun kama su ba tare da ko kwarzane a jikinsu ba, aka dauke su zuwa Barikin Sojoji na Basawa, lokacin da muka bukaci su ba mu su, sai suka ki, suka ce su ne za su kai su asibitin Shika, don haka mu je mu dauke su a can, daga baya ne muka samu labarin sun kashe Ahmad da Hameed, Ali kuma ya samu rauni a kafa. Ya samu mummunar karaya, ba na tsammanin raunin harsashi ne. Sun karya masa kafa ne. Har zuwa yanzu ba a dawo da shi gida ba, saboda sun tsare hanya.” Daga nan ya ci gaba da cewa “Ahmad yana karanta Kimiyyar Sarrafa Sinadarai a Jami’ar kere-kere a Shenyang a kasar China, Hameed kuma yana karanta Kimiyyar kerawa da gyara jirgin sama a Jami’ar dian a kasar China.
Don haka ya zama dole a bincikin wannan al’amarin da ya faru, don a hukunta duk mai laifi. Wani abu bayan wannan zai ci gaba da ririta wutar rikicin da ba a san karshenta ba. Abin bakin ciki ne a ce jami’an tsaro sun aikata haka ga ’yan Shi’a da suke kan gaba wajen yin Allah wadai da Boko Haram.
Ya kamata a nada kwamiti mai zaman kansa da zai binciki wannan al’amari, bai kamata a dora hakkin binciken a kan sojoji ba. A yanzu haka gwamnati tana ta fadi-tashin dawo wa al’umma kwarin gwiwa kan sha’anin tsaro, don haka ya kamata a bar binciken wannan al’amari a hannun Hukumar Kare Hakkin dan Adam, kamar yadda ta yi binciki batun wadanda aka kashe a Apo, inda jami’an tsaro suka ce wadanda aka kashen ’yan Boko Haram ne, amma bayan an yi bincike aka gane ba haka ba ne.
Ya kamata shugaban ’yan Shi’a ya ci gaba da kokari wajen kwantar da hankalin mabiyansa, hade da ba su umarnin ci gaba da bin doka da oda.
A gaskiya yayin muzahara ’yan Shi’a na rufe hanyoyi, inda hakan ke hana al’umma gudanar da ayyukansu na yau da kullum, don haka yana da kyau Sheikh Zakzaky ya fadakar da mabiyansa ’yancin sauran al’umma a lokacin da suke muzahara.