A binciko inda kudin fanshon mahafinmu ya makale -Yalwa Tafawa balewa
Babbar Sakatariyar Hukumar Yaki da Jahilci ta Jihar Bauchi, kuma daya daga cikin ’ya’yan marigayi Firayi Ministan Najeriya, Sa Abubakar Tafawa balewa, Hajiya Yalwa Abubakar Tafawa balewa, ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta biya iyalansu fansho da garatutin mahaifinsu wanda aka kashe shekara 50 da suka gabata.Hajiya Yalwa Tafawa balewa ta ce duk da cewa kowa […]
Babbar Sakatariyar Hukumar Yaki da Jahilci ta Jihar Bauchi, kuma daya daga cikin ’ya’yan marigayi Firayi Ministan Najeriya, Sa Abubakar Tafawa balewa, Hajiya Yalwa Abubakar Tafawa balewa, ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta biya iyalansu fansho da garatutin mahaifinsu wanda aka kashe shekara 50 da suka gabata.
Hajiya Yalwa Tafawa balewa ta ce duk da cewa kowa ya san cewa mahaifinsu ya rasa ransa ne bayan ya sadaukar da rayuwarsa wajen kwato ’yancin Najeriya tare da tabbatar da kasancewarta a sahun gaba a Nahiyar Afirka.
“Mahaifinmu Tafawa balewa da marigayi Sardaunan Sakkwato babu abin da suka bari a duniya sai gaskiya da rikon amana kuma abin da suka yi ga Najeriya har duniya ta nade babu wanda zai biya su sai Allah, amma muna mamakin yadda aka gaza biyan fanshon mahaifnmu duk da cewa dokar kasa ce ta ba da dama a biya wadannan hakkoki,” inji ta.
Hajiya Yalwa ta bayyana haka ne lokacin da take zantawa da wakilinmu a gidansu da ke Bauchi a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta kara da cewa sun samu labari cewa a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan an ware kudi domin biyansu hakkokin mahaifinsu amma daga bisani aka samu zagon kasa daga wajen ofishin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Anyim Pius Anyim.
“Mun samu labarin cewa a gwamnatance an fitar da kudaden amma daga bisani sai suka yi layar zana saboda haka muna kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa a gudanar da bincike kan yadda aka yi da kudin.
Iyalan marigayi Nnamdi Azikiwe sun samu hakkokin mahaifinsu a lokacin Shugaba Jonathan amma mu na Tafawa balewa ba mu samu ko sisin kwabo ba. Muna kira ga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta sanya baki domin gudanar da bincike kan lamarin domin kafafen watsa labarai da dama a shekarun baya sun rubuta cewa an biya dukkan hakkokin Tafawa balewa amma gaskiya babu wanda ya ba mu ko kwabo,” inji ta.