A biranen Chana takardun kudi ba su da amfani

A biranen kasar Chana, an samu wani canji a fannin tattalin arziki. Ba wai a fannin gine-gne, ko basussuka, ko kashe kudade ba. A’a, yana da alaka ne da yadda kasar ke kokarin daina amfani da takardun kudi. A manyan biranen kasar, ana amfani ne da wayoyin salula wajen biyan kudin duk abin da mutum […]

A biranen Chana takardun kudi ba su da amfani

A biranen kasar Chana, an samu wani canji a fannin tattalin arziki. Ba wai a fannin gine-gne, ko basussuka, ko kashe kudade ba. A’a, yana da alaka ne da yadda kasar ke kokarin daina amfani da takardun kudi.

A manyan biranen kasar, ana amfani ne da wayoyin salula wajen biyan kudin duk abin da mutum ya saya. A wajen sayar da abinci, mai tsaron shago zai tambaya ko kana amfani da Wechat ko Alipay, idan ba ka da su ne, sai ya tambayi kudi.

“Wannan yana daya daga cikin manyan ci gaba da aka samu a kasar Chana a ‘yan shekarun nan. A yanzu dai kasar Chana ce kadai ke da wannn cigaban,” inji wani mai suna Richard wanda shi ne Manajin Darakta na kamfanin GSR bentures. 

kasar Chana kamar yadda kididdiga ta nuna. A shekrar 2016, an yi amfani da waya wajen biyan kudin abin da aka saya na sama da dala  Triliyan 5.5, kamar yadda kamfanin tuntuba na IResearch na nuna.

A wannan yanayin, baki masu yawan bude ido da ’yan kasuwa suna shan wahalar gaske kuma samun damuwa wajen bude asusun ajiya a Bankin Chana wanda ya sa dole su mayar da wayoyinsu tamkar asusu.

Kuma hasashe na nuna cewa abin zai kara muni nan gaba musamman ga baki. Haka ma kamfanoni masu so su sayar da kayayyakin su a kasar Chana dole ne sai sun yi amfani da manhajar Alibaba da Tencent da sauran manhajojin biyan kudi na kasar, ko kuma ba za a iya biyansu ba bayan an saya kayan su. Hakanan kuma kamfanonin Chana da suke amfani da wadannan mahajojin suma dole su dage wajen fuskantar Facebook, Google da Credit card da sune suke tashe a wasu sassan duniyar.