A biya karamin ma’aikaci N615,000 ko a ga bacin rai —NLC

NLC ta bukaci a yi karin shekaru biyar a kan wa’adin yin ritayar ma’aikata

A biya karamin ma’aikaci N615,000 ko a ga bacin rai —NLC

Shugaban NLC, Joe Ajaero

Kungiyar kwadagon ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta kara mafi karancin albashi zuwa N615,000 ko kuma ta fuskanci Turai. 

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin ta yi karin shekaru biyar a kan wa’adin yin ritayar ma’aikata.

Shugaban Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajeaoro ya ce mafi karancin albashin N615,000 ne zai yi daidai da halin da ake ciki na matsin tattalin arzikin da tsadar rayuwa a kasar.

Joe Ajaero da takwaransa na Hadaddiyar Kungiyar Ma’aikata (TUC), Festus Osifo ne suka gabatar da wannan buƙata a dandalin Eagle Square da ke Abuja, yayin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya.

Sun bukaci gwamnati ta gaggauta kammala shirin aiwatar da sabon mafi karancin albashin kafin karshen watan Mayu.

Shuwagabannin kwadagon sun sun ce rashin aiwatar hakan zai haifar da fito-na-fito na tsakanin gwamnatin da ma’aikata a ƙasar nan.

A daren ranar Talata NLC ta bayyana karin 25% da 35% na albashin ma’aikata da gwamnati ta ayyana a matsayin “ɓata lokaci.”

A cikin jawabinsa na ranar Laraba, Kwamared Ajaero ya ce: “A wannan lokaci, ’yan uwa, ina so in sanar da ku cewa,  yanzu muka fara yakin neman gyaran mafi karancin albashin ma’aikata a ƙasar nan.

“Mun tabbatar da dukkan bangarori sun samu wakilci, kuma tattaunawa ta yi nisa. Mun gabatar da bukatarmu ta N615,000 a gaban abokan tattaunawarmu, yanzu su muke sauraro.

“Amma idan ba a kammala tattaunawa a kan mafi karancin albashi ba zuwa karshen watan Mayu, lallai za a ga abin da ba a so daga gare mu,” in ji Ajaero.

Shuaban na NLC ya kuma yi kira ga gwamnati da ta duba yiwuwar ƙara shekarun ritayar ma’aikata daga shekaru 60 zuwa 65 na hauhawa; ko kuma shekaru 40 a kan aiki, daga shekaru 35, kamar yadda aka yi wa malamai da alkalai.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos