A biya mutanen da jirgin soji ya kai wa hari a Sakkwato diyya —PDP

Jam’iyyar PDP ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta biyan diyya ga al’ummar jiragen soji suka kai wa hari a lokacin da suke fatattakar ’yan ta’adda a yankin Ƙaramar Hukumar Silame da ke Jihar Sakkwato

A biya mutanen da jirgin soji ya kai wa hari a Sakkwato diyya —PDP

Jam’iyyar PDP ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta biyan diyya ga al’ummar jiragen soji suka kai wa hari a lokacin da suke fatattakar ’yan ta’addan Lakurawa a yankin Ƙaramar Hukumar Silame da ke Jihar Sakkwato.

Jam’iyyar ta yi kiran ne a sako ta na ta’aziyya kan fararen hula suka jikkata da waɗanda suka gamu da ajalinsu a harin jiragen sojin a yankunan Gidan Sama da Rumtuwa da ke karamar hukumar.

Kakakin jam’iyyar ba kasa, Debo Ologunagba, a sanarwar da ya fitar kan harin kuskuren, ya buƙaci a gaggauta gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin tabbatar da amincin ’yan Najeriya da kuma kauce wa aukuwar hakan a nan gaba a yayin yaƙi da ’yan ta’adda.”

PDP ta jaddada goyon bayanta ga taki da ta’addanci, amma ta nuna muhimmancin kula da rayukan fararen hula.

“Irin haka ta faru a shekarar 2023 inda harin jiragen soji ya kashe fararen hula a Jihar Kaduna, ga shi kuma hakan ya maimaita kansa a 2024, don haka wajibi ne a ɗauki matakin hana ci-gabansa.

“Muna kira da a bayar da cikakkiyar diyyar waɗanda suka rasu tare da cikakkiyar kulawa da lafiyar waɗanda suka jikkata,” in ji sanarwar.

Duk da a kaka jam’iyyar ta buƙaci sojoji su ci gaba da ragargazar ’yan ta’adda domin muttsuke su a Najeriya.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota