A biya nakasassu alawus dinsu ko su koma bara – Sarki Sharada

Shugaban Gidauniyar Kanawa Foundation wacce ke kokarin samar da ilimi ga nakasassu, Alhaji Abba Sarki Sharada ya bukaci gwamnatin Jihar Kano ta rika biyan nakasassu mabarata kudin alawus na Naira dubu goma-goma kamar yadda ta alkawarta a lokacin da ta hana su yawon bara, ko kuma su koma barar.Alhaji Sarki Sharada ya bayyana haka ne […]

A biya nakasassu alawus dinsu ko su koma bara – Sarki Sharada
A biya nakasassu alawus dinsu ko su koma bara – Sarki Sharada

Shugaban Gidauniyar Kanawa Foundation wacce ke kokarin samar da ilimi ga nakasassu, Alhaji Abba Sarki Sharada ya bukaci gwamnatin Jihar Kano ta rika biyan nakasassu mabarata kudin alawus na Naira dubu goma-goma kamar yadda ta alkawarta a lokacin da ta hana su yawon bara, ko kuma su koma barar.
Alhaji Sarki Sharada ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Kano, inda ya nuna takaici kan yadda nakasassun da mabukata ba sa iya samun alawus dinsu. “A da kafin gwamnati ta zo da wannan batu na hana bara, takan bayar da alawus na Niara dubu dai-dai gare su, to sai dai yanzu ko wannan Naira dubu ba sa samu balle sabon alawus na Naira dubu goma-goma da gwamantin ta yi musu alkawari. Abin takaici shi ne kananan hukumomi da suke batun ba su da kudi, a haka suke biyan shugabannin siyasa na unguwanni Naira dubu bakwai-bakwai duk wata. Amma idan nakasassu suka je neman alawus dinsu sai a ce babu kudi. Idan sun je bara kuma a kama su,” inji shi.
Ya ce lokacin da gwamnatin baya ta hana bara sun goyi bayan shirin musamman da suka ji ta yi alkawarin bayar da alawus ga mabaratan, “Amma yanzu haka za mu janye goyon bayan matukar Gwamna Abdullahi Ganduje bai dauki matakin gaggawa a kan haka ba. Dole mutum ya bukaci abinci da abin sha da magani da sauransu. Babu yadda za a yi mutum ya zauna haka, don haka dole su koma bara saboda ba su da wata hanya ta samun abinci,” inji shi.
Malam Abba Sarki ya nuna takaici kan yadda gwamnatin Kano a karashin Gwaman Abdullahi Ganduje ke yi wa harkar nakasassu rikon sakainar kashi inda har yanzu bai nada mashawarcinsa a kan bangaren nakasassu ba kamar yadda aka saba a gwamnatocin baya ba.  “Idan har gwamanti ba ta yi wani abin da ya dace ba, to fa ba ta da zabi sai ta kyale almajiran su je su yi bararsu. Idan kuma ta ci gaba da kama su, to za mu dauki matakin shari’a a kanta da Hukumar Hisba da suke kama su. Saboda a matsayinsu na ’yan kasa suna da ’yancin fita don neman abin sanyawa a bakin salati.”