…A Borno kuma sun kwace garin Gwoza

’Yan kungiyar Boko Haram sun kwace garin Gwoza daya daga cikin manyan garuruwan Jihar Borno, kamar yadda mazauna garin da wani jami’in tsaro suka tabbatar.Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, daruruwan mayakan Boko Haram dauke da bindigogi da kakin soja sun yi jijjifin mamaye garin da ke tsakanin duwatsu a shekaranjiya Laraba a cikin motocin […]

…A Borno kuma sun kwace garin Gwoza
…A Borno kuma sun kwace garin Gwoza

’Yan kungiyar Boko Haram sun kwace garin Gwoza daya daga cikin manyan garuruwan Jihar Borno, kamar yadda mazauna garin da wani jami’in tsaro suka tabbatar.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, daruruwan mayakan Boko Haram dauke da bindigogi da kakin soja sun yi jijjifin mamaye garin da ke tsakanin duwatsu a shekaranjiya Laraba a cikin motocin yaki da a kori kura suna zazzagayawa inji mazauna garin.
An ce sun kai farmaki garin a ranar Talata amma sojoji suka fatattake su, washegari Laraba da misalin karfe 4:00 na asuba suka kaddamar da gagarumin hari suka kwace garin.
Wani ganau da ya buga wa manema labarai waya daga Gwoza ya ce ’yan bindigar sun fara fatattakar sojojin da ke tsaron garin suka kwace makamansu kafin su kai hari ga mutane garin da ke guduwa zuwa kan duwatsu don neman mafaka kamar yadda suka saba.
Wani mazaunin Gwoza ya shaida wa manema labarai daga maboyarsa a kan dutse ta amfani da layin kamfanin sadarwa na Orange mallakar kasar Kamaru cewa: “Mafi yawanmu muna kan duwatsu, kuma akwai yiwuwar an kashe da dama, amma daga kan duwatsu muna iya ganin ’yan Boko Haram suna yawo da tankokin yaki da wasu motoci sun nufi fadar sarki.”
Ya ce, “Na rasa abokina da muke gudu tare lokacin da harsashi ya same daga baya. Muna firgice ba mu san abin da zai same mu cikin dare ba, saboda daukacin garin ya fada hannun ’yan ta’adda,” inji mai kiran wanda bai so a ambaci sunansa.
Jaridar ta ce ta samu bayanin cewa sabon Sarkin Gwoza Alhaji Muhammed Timta ya tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba, a daidai lokacin da mutanen garin ke cike da tsoron ko maharan sun kama shi.
Wasu sassan na Gwoza musamman bayan duwatsun da suke kan iyaka da Kamaru tuni suke karkashin ikon Boko Haram, wadanda suka kwace garuruwan suka kakkafa tutocinsu tun cikin watan Yunin da ya gabata.
Sojoji ba su ce komai kan kwace garin ba zuwa hada wannan rahoto, amma sun taba alawashin za su fatattake su daga garin bayan harin watan Yuni.
Sannan wata majiya a hedkwatar ’yan sandan Borno ta tabbatar da cewa ’yan sanda suna sane da harin da kuma kwace garin Gwoza da maharan suka yi.
kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a garuruwan Jihar Borno duk da cewa tana karkashin dokar ta-baci sama da shekara daya, inda mahara suka kashe sama da mutum dubu 13 daga shekarar 2009.
Ko a shekaranjiya a birnin Washington na kasar Amurka, Shugaba Jonathan ya bukaci hadin gwiwar manyan kasashen duniya don yaki da Boko Haram da sauran kungiyoyi irinta a Nahiyar Afirka da sassan duniya.