A bude makarantu ranar 22 ga watan nan, kamar yadda gwamnati ta tsara, ko a kara dagawa?

kungiyar Likitocin ta kasa (NMA) ta yi soki matsayin da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta dauka na sanya ranar 22 ga watan nan a matsayin ranar da za a sake bude makarantun sakandare da firamare, bayan rufe su saboda tsoron yaduwar cutar Ebola. kungiyar ta bukaci a sake dage komawa makarantun har zuwa karshen shekarar […]

A bude makarantu ranar 22 ga watan nan, kamar yadda gwamnati ta tsara, ko a kara dagawa?
A bude makarantu ranar 22 ga watan nan, kamar yadda gwamnati ta tsara, ko a kara dagawa?

kungiyar Likitocin ta kasa (NMA) ta yi soki matsayin da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta dauka na sanya ranar 22 ga watan nan a matsayin ranar da za a sake bude makarantun sakandare da firamare, bayan rufe su saboda tsoron yaduwar cutar Ebola. kungiyar ta bukaci a sake dage komawa makarantun har zuwa karshen shekarar nan don kauce wa yaduwar cutar. Shin daukar wannan  matakin ya dace? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

 

Na goyi bayan a bude makarantu a ranar -Na Baban Yawo

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Abubakar Muhammad Na Baban Yawo:  A gaskiya na goyi bayan a bude makarantun firamare da na sakandare a ranar 22 ga watan nan da muke ciki kamar yadda gwamnati ta tsara don idan saboda tsoron kamuwa da cutar ebola ce aka ki bude su tun farko, to me za a ce game da makarantun Islamiyya da ke bude tun daga wancan lokaci kawo yanzu?  Su ba mutane ba ne suke karatu a cikinsu?  A matsayinmu na Musulmi mun san kaddara don haka bude makarantu da rashin bude su ba shi ne zai kawar da kamuwa da cutar ba, komai dai mukaddari ne.

 

Bude makarantun shi ne mafita -Tanimu Muhammad

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Tanimu Muhammad, Sakataren  kungiyar Agaji ta Jama’atu Nasril Islam reshen Jihar Kaduna: “Gaskiya zaman yara a gida a yanzu ba shi da amfani don haka bude makarantun shi ya fi dacewa don a cigaba da  yin karatu.  In ka lura da ma yankin Arewa an yi masa nisa a harkar karatun boko don haka idan gwamnati ta cigaba da barinsu a rufe don tsoron kamuwa da cutar Ebola har tsawon lokaci, harkar karatu zai kara tarbarewa a yankin Arewa. 

 

Bude su shi ya fi dacewa – Dokta Sa’idu Abubakar Musa

Daga Adam Umar, Abuja

Dokta Sa’idu Abubakar Musa: “Bude makarantun shi ya fi saboda zai taimaka wajen fadakar da yara a kan cutar. A ganina ba karamar koma baya ne a ci gaba da dakatar da bude makarantun firamare da sakadare da sunan magance yaduwar cutar Ebola, saboda ai ba’a hana jama’a haduwa a kasuwanni ba, ko a tashar mota, ko a wuraren ibada ba. Me ya sa za’a ci gaba da dakatar da makaranta wajen da a ke koyar da yara ilimin fanni daban-daban ciki har da na kiwon lafiya.

 

Cigaba da rufe su bai kamata ba

– Muhammad Gaji Isma’il

Daga Adam Umar, Abuja

Muhammad Gaji Isma’il: “A bude makaranta shi ya fi alheri saboda ai kusan kowa yanzu ya san dalilalan da suke haddasa cutar Ebola da kuma alamun wanda ke dauke da ita. Kuma ba na jin babban mutum ballantana yaro da ke dauke da cutar, zai samu kuzarin da zai iya zuwa makaranta, sai dai ya kamata a samar da na’urorin gwaji ga dukkan makarantu don hana dukkan wadanda ke dauke da alamar cutar, shiga cikin makaranta idan har sun iya zuwa makarantan.

 

Na goyi bayan kara wa’adi
– Alhaji Auwal Laleko

Daga Rabilu Abubakar, a Gombe

Alhaji Auwal Laleko: “A ganina bai kamata a bude makarantu a ranar 22 ga watan nan ba, har sai jami’an lafiya sun tabbatar babu wannan cutar ta Ebola saboda kar ayi gaggawan komawa. Ka ga anyi gudun gara, a tarar da zago. Tun da dama tun farko don Ebola ne aka rufe makarantun kuma yanzu
ba’a tabbatar cewa an kawar da cutar ba, me ya sa za’a ce ana son sake bude makarantun nan ba lokacin da aka tsara tun farko ba, a duba dai a gani.”

 

Bai dace a sake dagawa ba
– Ibrahim Baba Sulaiman

Daga Rabilu Abubakar, a Gombe

Ibrahim Baba Sulaiman: “A  ra’ayina bai kamata a sake dage hutun makarantun ba, kamata ya yi a koma a ci gaba da koyarwa domin idan taron ne ba’a so ai cunkoson yara ‘yan makaranta bai kai tarurrukan siyasa da na harkokin yau da kullum da ake gudanarwa ba a halin yanzu. Abinda ya fi shi ne a dalibai da malamansu su koma makaranta kawai a ci gaba da koyar da yara domin kada karatunsu ya tabarbare.”