A ceto makarantun almajirai na zamani

A kwanakin baya ne jaridar Daily Trust ta buga wani rahoto na musamman inda ta nuna makarantun almajirai na zamani da ake kira Tsangaya da tsohon Shugaban kasa Goddluck Jonathan ya assasa a lokacin mulkinsa na cikin halin kaka-ni-kayi. Makarantun, wadanda aka assasa da nufin samar da makarantun allo na zamani da zai rika amfani […]

A ceto makarantun almajirai na zamani

A kwanakin baya ne jaridar Daily Trust ta buga wani rahoto na musamman inda ta nuna makarantun almajirai na zamani da ake kira Tsangaya da tsohon Shugaban kasa Goddluck Jonathan ya assasa a lokacin mulkinsa na cikin halin kaka-ni-kayi. Makarantun, wadanda aka assasa da nufin samar da makarantun allo na zamani da zai rika amfani da manhaja irin na karatun boko da na tsarin karatun allo, an assasa ne da nufin magance matsalar jahilci da kuma rage yawan wadanda suke barin makarant a yankin Arewa.

Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya kaddamar da wadannan makarantu na zamani a garin Gagi na Jihar Sakkwato a ranar 10 ga watan Afrailun shekarar 2012. Sannan kuma ya yi wa dalibai 25 rajista a sabuwar makarantar ta Gagi, wadda ita ce ta farko a irin wadannan makarantu. Kuma makarantar wadda ta kwana ce, kuma tana da ababen karatu na zamani kamar dakunan karatu, ajujuwan karatu, wajen koyon sana’o’i, dakunan kwana, wajen cin abinci, asibiti da kuma gidajen malamai. Sannan kuma an kasafta kashe Naira biliyan 15 domin wannan aikin.

Amma bayan shekara biyar da fara aikin, da yawa daga cikin wadannan makarantun an mayar da su makarantun boko zalla, sannan kuma wasu da yawa daga cikinsu sun lalace. Misali, Makarantar Tsangaya ta zamani da aka gina a karamar Hukumar Talatar Mafara a Jihar Zamfara, an mayar da ita Makarantar Sakandare ta kimiyya (Command Science Secondary School). Kwamishinan Ilimin Jihar Zamfara, Mukhtar Lugga ya ce an mayar da makarantar ta zamani zalla ne saboda gininsu na rubewa.

A Jihar Sakkwato, makarantar Tsangayar da aka kaddamar a shekara biyar da suka wuce da dalibai 260 a matsayin dalibai na farko, yanzu dalibai kadan ne ke zuwa makarantar. Bakwai daga cikin ajujuwa 10 na makarantar yanzu babu dalibai a cikinsu.

A Jihar Kaduna, makarantun Tsangayar na fama da matsalolin rashin malamai, kayan aiki, da kazanta.

A makarantun Tsangaya guda hudu na Jihar Bauchi, dakin gwaji, wajen koyon sana’o’i da asibitocin makarantun ba sa aiki, kuma ba a taba sa musu kayan aiki ba. A Jihar Kano kuma, Makarantun Tsangaya suna aiki ne kamar makarantun kudi, domin da kudin da dalibai ke biya na kungiyar Malamai da Iyayen dalibai ne ake amfani wajen kula da makarantar kamar magani da dai sauransu. A Jihar Kebbi, daliban makarantar Tsangaya da ke anguwar Tudun Wada, ana tura su su je su yi bara a kan titi.

Marigayi Umaru Musa Yar’adua ne fara tunanin assasa irin wadannan makarantu na Tsangaya, a lokacin da ya kafa wani kwamitin ministoci da za su ziyarci kasar Indonesiya domin su ga yadda ake gudanar da makarantun Madrash. A lokacin da Barista Nyesom Wike ya maye gurbin Farfesa Rukayyatu Rufa’I a matsayin minsitan Ilimi, sai ya sanya siyasa a cikin lamarin na gina makarantun na Tsangaya, inda ya gina makarantar Tsangaya a Jihar Ribas, sannan kuma ya gina wani a Jihar Neja bayan gwamnatin Jihar Ebonyi ta ki amincewa a gina a jihar. Dukan wadannan makarantun da an gina su ne a jihohin da suka fama da matsalar yawan almajirai. Sannan kuma an yi amfani da kudaden da aka kasafta domin karatun Tsangaya wajen yin wasu ayyukan daban.

Gwamnonin jihohin Arewacin kasar nan ne ya kamata a fara nuna wa yatsa a kan tsaikon da aka samu wajen samar da wadannan makarantu kafin Gwamnatin Tarayya.

Na daya dai wannan matsalar a yankin Arewa ne ya fi kamari. Na biyu kuma, bayar da ilimi a karkashin tsarin makarantun Tsangaya ya fado ne a karkashin ilimi a matakin farko wanda nauyin ne da ya rataya a wuyan jihohi da kananan hukomomi. Wadannan dalilan ne suka sa gwamnonin jihohi Arewa suka fi zama masu laifi wajen shiriricewar shirin. Yawancin gwamnonin Arewa ba su damu da shirin ba. Wadansu daga cikinsu, saboda siyasa, sai suka kai makarantun yankunan da bai dace ba, wasu kuma suka ki dabbaka shirin, domin shirin bai da wani riba mai gwabi a siyasance.

Ya kamata gwamnoni su san cewa Almajirai suna bukatar tallafin gwamnati, domin suma kamar sauran yaran Najeriya, dole ne a basu ilimi. Sun cancanci a koyar da su a makarantun Tsangaya na zamani da kudaden jiha domin suma su amfani al’umma, baya ga irin yadda suka zabi su yi karatu. Muna kira ga Gwamnatin Tarayya ta farfado da wannan shirin tallafin na karatun Tsangaya ta hannun kwamitin tabbatar da ayyuka na kasa da ke aiki tare da Hukumar Kula da ilimi a matakin farko (UBEC). Muna kuma kira ga gwamnonin jihohi da su cire siyasa wajen yin kasafin kudin da ya dace da zai taimaka wa tallafin da suka karba daga Gwamnatin Tarayya.