A ci gaba da addu’o’in zaman lafiya – Limamin Minna
Babban Limamin Minna Sheikh Ibrahim Isah Fari ya bukaci al’ummar kasar nan su kara taimakawa da addu’o’i tare da rokon Allah Ya kawo kan karshen matsalar tsaro da ta addabi shiyyar Arewa maso Gabas da ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi da suke jefa jama’ar yankin cikin mawuyacin hali.Sheikh Ibrahim Fari ya ce halin da […]
Babban Limamin Minna Sheikh Ibrahim Isah Fari ya bukaci al’ummar kasar nan su kara taimakawa da addu’o’i tare da rokon Allah Ya kawo kan karshen matsalar tsaro da ta addabi shiyyar Arewa maso Gabas da ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi da suke jefa jama’ar yankin cikin mawuyacin hali.
Sheikh Ibrahim Fari ya ce halin da kasashen Musulmi suka shiga abin takaici ne ganin yadda a kullum ake rasa rayuka musamman yankin Falasidinu da suke ta fafutikar kwato yankin daga mamayar kasar Isra’ila da ke samun goyon bayan kasashen Yamma da Amurka.
Babban Limamin ya nemi al’ummar Musulmi su ci gaba da sadaukar da rayukansu kamar yadda Annabi Ibrahim ya bi umurnin Allah, ya sadaukar da dansa Isma’il, a karshe Allah Ya sauya masa da abin yanka mai girma.
A jawabin Gwamnan Jihar Neja Alhaji Mu’azu Babangida Aliyu ya nemi al’umma su gode wa Allah da Ya nuna musu wannan lokaci na Eid-el-Kabir a daidai lokacin da kasar ta cika shekara 54 da samun ’yancin kai. Kuma su ci gaba da yi wa shugabbni da kasar addu’o’in samun nasara da bunkasar arziki.
Gwamna Babangida Aliyu ya ce akwai bukatar Musulmi su yi amfani da darussan wannan lokaci domin wanzar da zaman lafiya a tsakanin jama’a, kuma wadanda Allah Ya wadata su mayar da hankali wajen taimaka wa wadanda ba su samu damar yin layya ba.
Gwamnan ya yi kira ga ’yan Najeriya su yi wa alhazan kasar nan addu’ar dawowa gida lafiya bayan da suka cika umurnin Allah na gudanar da aikin Hajjin bana.