A ci gaba da dabbaka darussan Ramadana – Limamai

Babban limamin masallacin Izala na Kuros Ribas, Assehik Bashir Salihu Abuga ya jagoranci dimbin  Musulmi  a wajen sallar Idi, tare da takwaransa na kungiyar Fityanul Islam,  Assheik Garba Dandalin Turawa Kano, shi ma a filin Idi da ke harabar jami’ar Kalaba, da misalin karfe tara da rabi na safe . Bayan kammala sallar Idi Assheik […]

A ci gaba da dabbaka darussan Ramadana – Limamai
A ci gaba da dabbaka darussan Ramadana – Limamai

Babban limamin masallacin Izala na Kuros Ribas, Assehik Bashir Salihu Abuga ya jagoranci dimbin  Musulmi  a wajen sallar Idi, tare da takwaransa na kungiyar Fityanul Islam,  Assheik Garba Dandalin Turawa Kano, shi ma a filin Idi da ke harabar jami’ar Kalaba, da misalin karfe tara da rabi na safe .
Bayan kammala sallar Idi Assheik Salihu Abuga ya bayyana wa Aminiya takaitaccen bayanin da hudubarsa t a kunsa kamar haka “ ta nuna godiya ga Allah (s.w.t.) da ya ba mu ikon kammala wannan babbar ibada ta azumin watan Ramadan, da abin da ya kunshi cikinsa na tsayuwa cikinsa , zuwa wajen tafsiri da kuma duk wasu ibadu na neman yardar Allah da kuma taimaka wa marasa karfi da mabukata.”.
Malamin ya ci gaba da bayanin abin da ta kunsa: “Ta yi bayanin mu kara dagewa, mu inganta Imanin mu, inganta Imani shi ne asasi na komai, idan aka inganta Imani Allah yana karbar ayyukan mu nagari, amma idan Imani bai inganta ba baya karbar ayyuka nagari, yana da muhimmancin inganta akida da yin aiki saboda Allah da kara jajircewa kan yi wa Allah da’a , da kuma nisantar abin da ya hana, to a nan ake samun taimakon Allah, idan kuna son Allah ya taimake ku. To  kin  yi wa Allah da,a da manzon sa.” Sanna kuma da tabbatar da inami nisantar saba umarnin Allah da ManzonSa da inganta akida nisantar saba wa Mahalicci .
Har wa yau ta yi bayani kan: “Haka nan kuma ta yi akan mahimmancin hada kai misali halin da muke cikin a kasar nan, musamman ma al’ummar Musulmi, kuma mu ma mun san abin da ke tsakanin mu,  ai akwai wadanda Allah ya yi bayani akan su, idan ba mu yi koyi da su ba, to za a samu fitina a bayan kasa, bayan haka ta nuna mahimmancin idan zabe ya zo mutum ya yi katin jefa kuri’a da katin shaidar dan kasa da ake yi halin yanzu ko ina cikin kasa.  Kowa ya tabbata ya mallake shi, ranar zaben nan aji tsoron Allah, kuma a zabi shugaba nagari  da nuna mahimmancin tashi tsaye mu yi addu’a, tare da taimaka wa marasa galihu da ziyartar marasa lafiya da kuma fitar da zakkar kono.”inji shi
Assheik Garba Dandali , a tasa hudubar ya yi bayanin yadda Musulmi ya dace su kara hada kai da kuma neman zaman lafiya, su ci gaba da nuna juriya da hakuri bisa dukkan  al’amuran addini da kuma rayuwa, inda ya nuna mahaimmancin dabbaka darussan da watan Ramadan day a shude ga kowane Musulmi.