A ci gaba da kiran Gwamna Almakura ya yi takara

A shekarar 2011 al’ummar Jihar Nasarawa sun fito kwansu da kwarkwata zuwa rumfunan zabe don su zabi wadanda za su shugabancesu. Amma sai ya kasance kadan daga cikinsu ne ke da masaniyar sakamakon zaben zai sauya alkalar jagorancin jihar daga hannun tsohon gwamnan jihar karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Aliyu Akwai Doma zuwa hannun gwamna […]

A ci gaba da kiran Gwamna Almakura ya yi takara
A ci gaba da kiran Gwamna Almakura ya yi takara

A shekarar 2011 al’ummar Jihar Nasarawa sun fito kwansu da kwarkwata zuwa rumfunan zabe don su zabi wadanda za su shugabancesu. Amma sai ya kasance kadan daga cikinsu ne ke da masaniyar sakamakon zaben zai sauya alkalar jagorancin jihar daga hannun tsohon gwamnan jihar karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Aliyu Akwai Doma zuwa hannun gwamna mai ci yanzu, karkashin inuwar jam’iyyar APC Umaru Tanko Almakura. Wani abin da za a iya bayyana a matsayin farin ciki da annashua, shi ne, yadda sakamakon zaben ya bada damar kamun ludaynin sabuwar gwamnatin Umaru Tanko Almakura karkashin rusasshiyar jam’iyyar CPC da yanzu ya narke zuwa APC. Da hawansa kan karagar mulki a ranar 29 ga Watan Mayun shekarar 2011, Gwamna Umaru Tanko Almakura ya fara aiki gadan-gadan, domin kyautatawa tare da inganta rayuwar al’ummar jihar baki daya. 

Shekaru uku da rabi ke nan yau, Gwamna Umaru Tanko Almakura ya cika dukka alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabe. Al’ummar Jihar Nasarawa dai sai sambarka, Jihar Nasarawa sai walkiya take yi kullum, ta canja kama mai kyau. Babu shakka dimbin ayyuka da gwamnan ke yi suna dadada wa al’ummar jihar baki daya, musamman talakawa da ma, wadanda suka yi la’akari da namijin kokari da yake yi na cika dukka alkawura da ya yi.
Da ikon Allah ya canja fatsalin jihar cikin wadannan shekaru uku da rabi da ya yi akan mulki sabanin abin da ya wakana a shekaru 12 kafin ya hau karagar malki a matsayin gwamna. A yunkurinsa na sanya farin ciki a zukatan mutane, musamman marasa galihu, Gwamna Almakura ya kawo dauke wurin gyaggyara al’amura, domin gina sabuwar Jihar Nasarawa, inda ana iya kididdige nisan kilomita a hanyoyin da ya yi kamar yadda bangarorin kiwon lafiya da fannin noma da ilimi da ayyukan gwamnati da dai sauransu da dama, duk sun bunkasa. Sakamakon ayyukan da gwamnan ke gudanar a jihar babu kama hannun yaro ne, ya sanya soyayyarsa ta shiga zukatan al’ummar jihar da ma wajenta, don suna ganin ayyuka na gudana cikin tsari. Shi ya sa ma idan za a iya tuwana kwanakin baya, a lokacin da wasu ’yan majalisar dokokin jihar suka yi yunkurin tsige shi babu gaira, babu dalili, al’ummar jihar suka fito kwansu da kwarkwatarsu, wadanda galibi talakawa ne, suka nuna adawarsu da yunkurin ‘yan majalisanr, inda suka gudanar da zanga-zangar lumana a ciki da wajen jihar, suka kuma yi kira ga ‘yan majalisar da su mayar da hankularsu wajen biya bukatun al’ummomin yankuna da suke wakilta maimakon su rika zargin gwamnan da suka bayyana a matsayin mai adalci da ba a taba yin gwamna irinsa ba ba gara ba dalili. Duk da cewa kudin shigar jihar bas hi da yawa, yana gudanar da ayyukan ci gaba cikin gaskiya da rikon amana. Don kuwa ana iya ganin haka a kasa wajen samar da abubuwan more rayuwa, sabanin yadda aka karkatar da akalar dukiyar al’umma zuwa aljihun wasu mutane ‘yan kwashe-ka ruga da aka yi a baya.
Wani daga cikin bangarorin da gwamnan ke taka rawar gani kuma shi ne bangaren tabbatar da tsaro a jihar. Ko da yake gwamnan ya gaji rigingimun kabilanci a jihar daga gwamnatocin da suka shude, amma ya gudanar da tarurruka da dama, inda ya hado dukkan kabilun da ke fada da junansu a jihar, wadanda suka hada da Tibi da Eggon da Alago da Gwandara da Migilli da dai sauransu; yana kuma tallafa wa wadanda rigirgimun ya rutsa da su, ta hanyar samar musu da abinci da sutura da sauran kayayyakin agaji.
A ‘yan kwanakin nan nema gwamnan ya gayyato dimbin masu gudun hijiran daga sassan jihar zuwa babban dakin taron gwamnati (City-hall) da ke Lafiya fadar jihar, inda ya rarraba musu kayayyakin abinci da sutura da sauransu, sannan ya tabbatar musu cewa nan ba da jimawa ba gwamnatinsa za ta fara kwasarsu zuwa gidajensu, ta kuma turo musu jami’an tsaro da za su tare da su na tsawon lokaci, don kare lafiyarsu da dukiyoyinsu. Saboda wadannan ayyuka da wasu da dama ne ma al’ummar jihar ke yawaita kiraye-kiraye cewa gwamnan ya sake tsayawa takara a shekarar 2015.
Sannan Almakura ya sanya al’ummar jihar fifiko tare da jerin-faran-dango wajen yin kiraye-kirayen da ya amsa kiranye-kirayen mutane ya tsaya takarar a shekara mai zuwa. Alal misali, a ‘yan kwanakin nan ne shiyar dattawa ta Arewa a jihar da ta kunshi kananan hukumomi uku da suka hada da Akwanga da Wamba da Nasarawa-Eggon su ne suka fara assasa jerin gwanon tare da kiran gwamnan ya sake tsaya takara. Domin nunawa karara cewa da gaske suke yi al’ummar wannan yanki, sun ma riga malam shiga masallaci, inda suka saya masa takardar bayyana aniyar tsayawa takarar, suka kuma yi ikirarin cewa idan ya ki ya ba da kai bori ya hau, to dimbin jama’ar da ke kiran sa ba za su yi wata-wata ba wajen maka shi a kotu.
Su ma al’ummar shiyyar Keffi da Nasarawa da kuma Toto sun yi dafifi a garin Keffi kwanakin baya, inda suka gabatar da bukatarsu wajen ganin gwamnan ya yanki takardar tsayawa takarar gwamnan mai zuwa.
Al’ummar shiyar lafiya da ta kunshi karamar Hukumar Obi da Doma da Lafiya fadar jihar ba a barsu a baya ba, don su ma sun gabatar da bukatarsu na ganin ya sake fito takara a shekarar 2015 don ya ci gaba da kyawawan ayyukan raya kasa da yake gudanarwa a jihar da ma kasa baki daya. Saboda wadannan da sauran kiraye-kirayen da mafi yawan al’ummar jihar ke yi wa gwamnan ya sake fitowa takara a shekarar 2015. Babu shakka yana da mahimmanci gwamnan ya sake tsayawa takarar, domin amsa kiran wadannan dimbin jama’ar jihar da ma kasa baki daya, wadanda ke yaba wa kyawawan ayyukansa ke yi.
A na su bangaren al’ummar jihar ga dukkan alamu sun yi imanin cewa gwamnan ne kawai zai iya share musu hawaye, ya ci gaba da samar musu da ribar dimokuradiyya a kowane fannin rayuwa. Kodayake ba wai gwamnan ne kadai zai iya warware matsalolin jihar baki daya har abadan ba, kasancewa wa’adinsa takaitacce ne. Amma a halin yanzu shi ne kadai zai iya kai ta tudun-mun tsira.
Bisa la’akari da dimbin alfanun da na jero, ina ganin duk mai hankali zai iya yarda da cewa akwai bukatar daukacin al’ummar jihar Nasarawa su manta da bambance-bambancen kabilanci ko siyasa da ke tsakaninsu, su kuma mai da wukakensu cikin kube, su fito kwansu da kwarkwata don zaben gwaninsu a shekarar 2015. Da zarar ya amsa kiran don ba shi damar, hakan ba zai yiwu ba, idan ana ci gaba da kashe-kashe a tsakanin kabilu daban-daban da ke jihar. Dole al’ummar jihar su yi sulhu a tsakaninsu su yafe wa juna, don hakarsu ta cimma ruwa, su sadaukar da komai har ma da rayukansu, don ganin cewa jihar ta samu ’yancin kanta don ta bunkasa, kamar sauran jihohin kasar nan da aka kirkiro a lokaci daya da jihar. Uwa-uba mu dage da addu’a Allah Ya zaba mana shugabanni nagari, akowane mataki,don mu samu kyakkyawan wakilci a jiha da tarayya.

Wada ya rubuto makalarsa ne daga Lafiya, Jihar Nasarawa.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya