A ci gaba da yi wa Buhari addu’ar nasara – Sardaunan Goron Na-Maye

Malam Abubakar Abdullahi Goron Na-Maye, Malamin addinin Musulunci, Sardaunan Goron Na-Maye, Talban Maradun, Hakimi a masarautar Zamfara, a zantawarsa da manema Labarai a Kaduna, ya shawarci zabbabun shugabanni kan yadda za su jagoranci jama’ar da suka zabe su. Kuma ya ce akwai bukatar jama’a su ci gaba da yi wa Buhari addu’ar samun nasara: Aminiya: […]

A ci gaba da yi wa Buhari addu’ar nasara – Sardaunan Goron Na-Maye
A ci gaba da yi wa Buhari addu’ar nasara – Sardaunan Goron Na-Maye

Malam Abubakar Abdullahi Goron Na-Maye, Malamin addinin Musulunci, Sardaunan Goron Na-Maye, Talban Maradun, Hakimi a masarautar Zamfara, a zantawarsa da manema Labarai a Kaduna, ya shawarci zabbabun shugabanni kan yadda za su jagoranci jama’ar da suka zabe su. Kuma ya ce akwai bukatar jama’a su ci gaba da yi wa Buhari addu’ar samun nasara:

Aminiya: An kammala zabuubuka a kasar nan lafiya, a matsayinku na iyayen al’umma wane jan hankali za ka yi wa jama’a a kan yadda suke nuna murna da farin cikinsu?

Sardaunan Goron Na-Maye: Godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Idan muka yi la’akari da irin abubuwan da suka faru a baya, babu shakka malamai sun yi tarayya wajen ilimantar da jama’a, a kan a gudanar da addu’o’i domin Allah Ya kawo mafita da kuma sauki a cikin wannan zabe, kuma kamar yadda kowa ya gani Allah Ya amshi addu’o’in jama’a an yi zabe lafiya an kuma kammala lafiya. Saboda haka wannan babban abin farin ciki ne ga dukkan ’yan Najeriya domin su gode wa Allah Mahallici a kan wannan baiwa da Ya yi musu, wanda idan muka gode to babu shakka Allah zai kara mana. Sannan abu na gaba shi ne Allah Ya tanadi hanyoyin da dan Adam zai bi wajen nuna godiyarsa ga Allah, daga cikin wadannan hanyoyi akwai mutum ya yi sujuda ga Allah ko ya yi Sallah ta nafila ko ambaton Allah ta fadin alhamdulillah, ko yin sadaka da sauran abubuwa na alheri da dama wadanda za ka bayyana godiyarka ta samun wata nasara, sabanin irin abubuwan da muka ga sun faru a ’yan kwanakin baya, musamman yadda samari suka rika wasanni da ababen hawa lamarin da ya kai ga jin raunuka da rasa rayuka. To a magana ta gaskiya Allah ba Ya son haka, kuma ba ta haka ake nuna godiya ga Allah ba. Sannan wani karin abin bakin cikin shi ne yadda wasu suka rika barnata motocinsu na alfarma, Allah Ya yi maka baiwar da bai yi ma waninka ba maimakon ka gode maSa sai ka zo kana wulakantar da ita, saboda haka kiran da muke yi ga jama’a shi ne idan Allah Ya sanya aka samu wata nasara da ake nema, to akwai hanyar da ya kamata a bi wajen nuna farin ciki da yin amfani da ni’imar domin kada wannan ni’ima ta gushe.
Aminiya: Ta bangaren shugabannin da suka yi nasara a zabe ko akwai wata shawara ko kira da za ka yi gare su?
Sardaunan Goron Na-Maye: Bayan Allah Ya nufi mutum da zama shugaba wata nasarar ita ce Allah Ya albarkace shi da wasu abubuwa guda uku. Abu na farko sh ine Allah Ya azurta shi da lafiya ta jiki wacce za ta taimaki mulkinsa, sannan abu na gaba Allah Ya nufe shi da kasancewa mai kyakkyawar niyya ta yin adalci ga jama’arsa, sannan abu na karshe Allah Ya taimake shi da samun mataimaka na kwarai.
Annabi (Mai tsira da amincin Allah) yana cewa: “Idan Allah Ya yi nufin sanya wa wani shugaba alheri a cikin sha’aninsa sai Ya samar masa da mataimaka nagari, domin idan ya mance wani alkawari da ya yi wa jama’arsa sai su tuna masa, haka nan idan shi ne ya tuna wani alkawari da ya yi wa jama’arsa sai su karfafe shi. Sannan idan Allah ba Ya nufin wannan shugaba da alheri sai ya ba shi miyagun mataimaka, ya zamana idan ya manta alkawari ba za su tuna masa ba, idan ya tuna ba za su karfafe shi ba.”
Saboda haka babbar fatar da muke yi wa wadannan shugabanni shi ne Allah Ya nufe su da kasancewa masu adalci, sannan Allah muke roko da Ya ba su mataimaka na kwarai, domin mataimaka na kwarai su ne ke bayar da kyawawan shawarwari a siyasance da kuma a aikace.
Aminiya: Talakawa fa, wacce kira ko shawara za a ba su?
Sardaunan Goron Na-Maye: Wato da farko ya kamata jama’a su gane cewa wadanda suka yi nasarar zaben nan, za su karbi mulki ne a wani yanayi na rashin kudi a asusun gwamnati wasu jihohin ma sun gaza biyan albashi, saboda haka za su amshi mulki ne a wani yanayi na rashin kuci. A baya can bisa ga al’adar jama’armu idan wani naka ya samu mulki to za ka yi ta farin ciki ne cewa mun haye, to, ya kamata ka fahimci bambancin wannan lokaci da lokutan da suka gabata, saboda haka sai an yi musu hakuri tukun har su samu gyara halin da ake ciki.
Sannan kamar yadda na yi bayani a wa’azi da na yi a wata Juma’a shi ne, addu’o’in da aka yi a baya har gwamnatin nan ta kai ga cin nasara ya zuwa yanzu an bar wadannan addu’o’i da kusan kashi 90, wannan ba karamin koma-baya ba ne, saboda haka ina kira ga jama’a cewa kada a tsaya wajen ci gaba da addu’a har zuwa ranar da za a rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari. Bayan nan kuma a ci gaba da yi musu addu’a Allah Ya yi musu jagora a kan mulkinsu, jama’a su sani cewa duniya gaba daya ta sanya ido a kan Najeriya bisa ga batun canjin nan da aka yi. Saboda haka idan aka samu nasara to dukanmu ne muka samu nasarar, sannan Allah Ya kiyaye a samu akasi, dukkanmu ne.