A cikin kwanaki hudu muna iya hada makamashin Nukiliya – Iran
Shugaban shirin hada makamashin Nukiliya na kasar Iran ya ce kasar za ta iya hada makamin Nukiya a cikin kwana hudu idan har kasar Amurka ta karya yarjejeniyar da kasar ta kulla da ita da wasu manyan kasashe a shekarar 2015. Ali Akbar Salehi, shugaban Hukumar Makamashi Mai linzami na kasar ne ya sanar da […]

Shugaban shirin hada makamashin Nukiliya na kasar Iran ya ce kasar za ta iya hada makamin Nukiya a cikin kwana hudu idan har kasar Amurka ta karya yarjejeniyar da kasar ta kulla da ita da wasu manyan kasashe a shekarar 2015.
Ali Akbar Salehi, shugaban Hukumar Makamashi Mai linzami na kasar ne ya sanar da hakan a daidai lokacin da ake tunanin cewa akwai baraka tsakanin kasashen guda biyu kan yarjejeniyar Nukiliyar da suka kulla, kamar yadda kafar yada labarai na Times of Israel ta ruwaito.
kasar Iran ta dauki alkawari cewa ba za ta karya alkawarin ba, bayan ta yanke shawarar ajiye shirin hada makamashin Nukiliya, domin a cire mata takunkumin da aka kakaba mata. Amma sai dai kuma yadda kasar Amurka ke yi wa yarjejeniyar gyaran fuska a yanzu na nema ya tayar da zaune tsaye.
“Za mu iya kai wa ga kashi 20 cikin 100 na habbaka Uranium a cikin kwana hudu a masana’antar makamashinmu na Fordo, amma ba ma so mu karya yarjejeniyar makamashin Nukiliya da muka shiga,” inji Salehi.
Sannan ya kara da cewa kasar Iran ba za ta amince hukomar kula da makamashin Nukiliya ta duniya su shiga masana’antar mu ba, domin hakan bai cikin yarjejeniyar da muka kulla.
“Mun yi magana a kan sashi na T, sannan kuma matsayarmu a bayyana yake,” inji Salehi, inda yake nuni da wani sashen yarjejeniyar da suka kulla.
Ita dai wannan yarjejeniyar, an kulla ta ne da tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, inda aka bukaci kasar Iran ta ajiye shirin hada makamashin Nukiliya.
Shugaba Trump ambaci kin amincewa da Tehran ta yi a duba sansanonin sojinsu a matsayin daya daga cikin hanyoyin bijirewa yarjejeniyar, duk da cewa sun nuna cewa suna girmama yarjejeniyar a bayyane.
Salehi ya yi jawabin kwanan nan ne bayan wani taro da ya yi da daraktan Hukumar Makamashin Nukiliya ta duniya (IAEA), Yukiya Amano a Tehran. Kuma shugaban hukumar ya gana da shugaban kasar Iran, Hassan Rauhani, da Ministan Harkokin wajen Iran, Mohammed Jabae Zarif, inda ya bayyana cewa a bangarensu, sun yi amanna cewa Iran na ci gaba da rike yarjejeniyar da aka kulla.
A na shi bangaren, Rauhani, ya ce Iran za ta ci gaba da hada makamai masu linzami domin tsaro, amma bai cikin alamomin watsi da yarjejeniyar.