A cikin mummunan ƙunci muka yi Sallar bana — Talakawa

Gwamna Buni ya roƙi Allah Ya karɓi duk ibadar da al’umma suka yi a cikin watan albarka na Ramadan.

A cikin mummunan ƙunci muka yi Sallar bana — Talakawa

Al’ummar Musulmi da suka gudanar da Karamar Sallar bana a ranar Laraba, sun ce sun gudanar da bukukuwan Sallar ce a cikin mugun kuncin da ba su taba samun kansu a ciki irin bana ba.

Sun shaida wa Aminiya cewa wasu daga cikinsu ko dinkin Sallah ba su iya yi wa ’ya’yansu ba, balle a yi maganar yi ka mata da su kansu.

Yayin da wasu suka ce hatta Zakkar Fid-da-Kai da ta wajaba a kan Musulmi babba da yaro a bana ba su samu damar yi ba saboda ƙuncin rayuwa da talauci da suka samu kansu a ciki, wanda suka dora wa janye tallafin man fetur da karya darajar Naira.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da shugabanni suke kira ga talakawan kan su ƙara sadaukar da kai tare da nuna soyayya ga juna don sake gina kasa.

Imam Hussaini Udawa da ke Jihar Kaduna ya shaida wa Aminiya cewa a tunda aka kafa Nijeriya ba a taba shiga tsananin tsadar kayan abinci ba irin wanda ake ciki a yanzu, musamman a lokacin hidimar Sallah.

Ya ce hatta azumin watan Ramadan ma a cikin tsananin rayuwa talakawa suka yi ballantana bikin Karamar Sallah.

Sai dai malamin ya yi godiya ga Allah da Ya sa aka yi azumi da Sallar lafiya kuma a cikin koshin Lafiya.

Ya ce, “A yi hakuri mu gode wa Allah da halin da muka tsinci kanmu a ciki. Domin a gaskiya tun da aka kafa Nijeriya ba na tsammanin an taba yin tsadar kayan abinci da nama da sauransu a lokacin Sallah kamar yadda aka yi a bana.

“Duk inda ka je talakawa kuka suke yi saboda sadakar ma da ake yi a da, a yanzu an dai na yi,” in ji shi.

Sai ya shawarci al’umma cewa duk da tsadar rayuwa da su daure su yi Zakkar Fid-da-kai domin a cewarsa akwai lada mai yawa saboda Manzon Allah (SAW) ne ya ce a yi.

“Ko mutum riga uku ke gare shi, yana da kyau ya sayar da ɗaya domin yin Zakkar Fid-da-kai saboda akwai lada mai yawa ga duk wanda ya yi,” in ji shi.

Umar Ramalan magidanci ne mazaunin Badarawa/Malali Kaduna, ya ce hakika Sallar bana ta zo masa da matsaloli da yawa, amma ya gode wa Allah tunda yana da rai da lafiya.

Ya ce a shekarun baya a ranar jajiberin Sallah za ka ga mutane na ta hada-hadar naman kaji ko na shanu da za a kai gida domin iyali su ci, amma a bana abin ba haka yake ba.

“A bana dai sai godiya, domin abin ba yadda aka saba ba. Yanzu abin da za a dafa a raba wa makwabta domin su ma su ci su san ana Sallah, babu ko kuma in ce ba a samu yadda ake so ba saboda kuncin rayuwa,” in ji shi.

Ya ce “Gaskiya akwai damuwa domin a yanzu akwai batun Zakkar Fid-da-Kai ko Zakkar Kono da ya kamata duk mai azumi ya fid da wa iyalansa.

“Amma ka ga a yanzu ba ta fid da kai ake ba, saboda ni ma ta kaina nake a yanzu.”

Aliyu Suleiman Zariya, mazaunin Kaduna cewa an yin hidimar Sallah daidai gwargwado domin abin da zai iya kurum ya yi saboda yanayin tsadar rayuwa.

Game da batun kayan Sallah musamman na yara, ya ce duk ya yi su kafin azumi ya kama domin samun sauki.

“Akwai kalubale duk da an aiwatar da wasu abubuwan. Wasu kuwa dole a yi hakuri. ’Yan uwa da abokan arziki ma hakuri ake ba su saboda yanayin da aka tsinci kai a ciki.

“Domin idan ka dubi fuskokin mutane za ka ga babu armashi saboda rashin kukd,” in ji shi.

Game da Zakkar Fid-da-Kai ya ce “Gaskiyar zance wasu ba za su yi ba domin yanayin da suke ciki. Akasarin mutane ta kansu suke yi.

“Wasu abincin da za su bayar ba su da shi kasantuwar an yi hidima da wanda suke da shi.”

Wani magidanci a garin Gombe Malam Ahmadu Adamu, ya ce yana da ’ya’ya shida, biyu mata da hudu maza amma ’ya’ya matan kawai ya iya yi wa kayan Sallah da taimakon ’yan uwa.

Ya ce, ba ya ma batun yi wa matansa, tun da ga shi ’ya’yan ma ba su samu ba saboda yadda kuncin rayuwa.

Malam Ahmadu, ya ce a halin da ake ciki ta abin da za a ci ake yi, ba ta ɗinkin Sallah ba domin sai an ci an koshi ake batun kayan Sallah sannan a yi batun Zakkar Fid-da-Kai.

Ya ce tunda yake bai taba ganin tsadar rayuwa irin ta wannan shekarar ba saboda kowa ta kansa yake yi taimako kuma ya yi kadan.

A cewarsa har zuwa lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ranar Litinin ba ya da abin da zai ci a gida ga kuma sana’arsa karama ce ta gyaran agogo da ba kowane lokaci ake samun aiki ba.

Sai ya ce da shugabanni suna da tausayi abi nda ya kamata su yi a watan azumi shi ne ciyar da al’umma musamman talakawa.

Ya ce amma a bana marayun da aka saba dinka wa kayan Sallah ma a kungiyoyi da daiddikun al’umma da yawan marayu da tsofin kaya za su yi Sallah.

Ku hada kai don gina kasa — Tinubu

A sakonsa na Karamar Sallah Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al’ummar kasar su hada kai, sannan su sadaukar da kansu a aikin gina kasa. masu gina kasa, kuma dole mu yi duk abin da ya kamata wajen bunkasa kasar nan.”

Shugaban, ya taya al’ummar Musulmi Sallar Eid-el-Fitr da ya kawo karshen azumin watan Ramadan.

Shugaban, ya yi kira a tabbatar da hadin kan kasa da nufin gina al’umma mai nagarta.

Ya ce wannan lokaci ne na mai da lamura ga Ubangiji, don haka ya kamata al’ummar kasa su dukufa wajen samar da hadin kai a tsakaninsu.

Shugaba Tinubu ta hannun Kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya yi addu’ar Allah Ya sa darussa da albarka da farin cikin da aka samu a watan Ramadan ya kasance tare da mu a koyaushe.

Ya yi wa ’yan Nijeriya fatan alheri da Barka da Karamar Sallah.

Yobe

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya taya al’ummar Musulmi murnar Sallah da samun nasarar kammala azumin watan Ramadan cikin koshin lafiya.

A wata takardar da aka raba wa manema labarai dauke da sa hannun Babban Daraktan ’Yan jarida da Yada Labarai na Gwamnan, Malam Mamman Mohammed, Gwamna Buni ya roƙi Allah Ya karɓi duk ibadar da al’umma suka yi a cikin watan albarka na Ramadan.

“Yayin da muke yin bukukuwan Karamar Sallah da ke nuna kawo karshen sauke wani rukuni na addini a wata guda, ina umartarmu da mu dauki darussa na sadaukarwa, kula da jin kan da ake nunawa a lokacin azumin watan Ramadan,’’ in ji Gwamna Mala.

Katsina

A saƙon Gwamna Dikko Umaru Radda na Jihar Katsina ga al’ummar jihar kan bikin Sallar kira ya yi ga Musulmi cewa, kada su manta da darussan da suka koya na hadin kai, tausayi da kaunar juna a watan Ramadan.

Ya ce “Yayin da muka yi ban-kwana da watan Ramadan, mu ci gaba da kasancewa masu tausayi, karamci da kyautatawa a rayuwarmu ta yau da kullum.

“Mu yi ƙoƙari mu zama mutane nagari masu haɗin kai da kaunar juna a tsakaninmu,” in ji Radda a wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Sakataren Yada Labaransa, Malam Ibrahim Kaula Mohammed.

Adamawa

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, gargadi ya yi ga al’ummar Musulmi kan su ci gaba da amfani da darussan da suka koya a watan Ramadan na sadaukarwa, da’a da kuma soyayya.

A wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaransa, Mista Humwashi Wonosikou, ya fitar ya, dole ne ’yan Najeriya su yi amfani da wannan lokaci wajen yin tunani da addu’a a kan irin halin da kasar nan ke ciki.

Kwara

Gwamnan Jihar Kwara, Shugaban Gwamnonin Nijeriya, Alhaji AbdulRahman AbdulRazak kira ya yi ga Musulmi da kada su yi watsi da koyarwar da suka samu a watan Ramadan.

A sakonsa na Barka da Sallah, Gwamna AbdulRazak ya ce, ya kamata Musulmi su mayar da hankali wajen ci gaba da aikata ayyukan alherin da suka yi a watan Ramadan kamar sadaka, kaurace wa munanan ayyuka da nuna kyawawan halaye.

Ya kuma bukaci al’umma su hada kai wajen kyautatawa tare da kauce wa duk wani abu da zai iya rushe ladan azuminsu.

Nasarawa

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya roki al’ummar Musulmi su ci gaba da dagewa wajen ci gaba da yin abin da azumin watan Ramadan ya koyar ta hanyar ci gaba da addu’o’i da tawakkali da samar da kyakkyawar alaka da juna a jihar.

Gwamna Sule, ya tabbatar wa al’ummar kasar nan cewa Jihar Nasarawa karamar Nijeriya ce mai dauke da al’ummu daban-daban daga kowane sashi na kasar nan, kuma ba tare da la’akari da kabila, yanki, addini ko akida ba, inda ya yi kira ga jama’a su kasance masu bin doka da oda.

Gombe

Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe kuma Shugaban Gwamnonin APC ya bukaci al’ummar Musulmi ne kan su ci gaba da amfani da darussan da suka koya a watan Ramadan na sadaukarwa da nuna soyayya ga juna.

A sakonsa na Eid-el-Fitr ga al’ummar, ya bukaci al’ummar Musulmi su jajirce da kara yin addu’o’i ga jihar da kasa baki daya, domin ganin an shawo kan kalubalen da kasar ke fuskanta.

Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi kuma Shugaban Gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed, a sakonsa na Sallah ya yi fatan alheri ga al’ummar Musulmi tare da tunatar da su a kan muhimmancin haɗin kai da nuna kauna ga juna.

Ya ce watan azumin Ramadan alama ce ta soyayya, kankan-da-kai da sadaukarwa, don haka ya zama wajibi ga Musulmi su sadaukar da kansu wajen yi wa jihar da kasa addu’a.

Ya buƙaci da kada su yi kasa a gwiwa wajen bayar da gudunmawarsu wajen ganin an samu zaman lafiya a jihar da kasa baki ɗaya daya.