‘A cire siyasa wajen nada jami’an kula da alhazai’

Wani malamin addinin Musulunci kuma tsohon Limamin Sojoji, Malam Abubakar Atiku Walin Kalgo ya shawarci gwamnatocin kasar nan su rika tura mutane masu tsoron Allah da tsare gaskiya a matsayin jami’an da za su rika yi wa alhazan Najeriya jagora a kasa Mai tsarki. Malam Abubakar Atiku ya yi wannan kira ne a lokacin da […]

‘A cire siyasa wajen nada jami’an kula da alhazai’
‘A cire siyasa wajen nada jami’an kula da alhazai’

Wani malamin addinin Musulunci kuma tsohon Limamin Sojoji, Malam Abubakar Atiku Walin Kalgo ya shawarci gwamnatocin kasar nan su rika tura mutane masu tsoron Allah da tsare gaskiya a matsayin jami’an da za su rika yi wa alhazan Najeriya jagora a kasa Mai tsarki.

Malam Abubakar Atiku ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Bunza da ke jihar, inda ya ce babbar matsalar da ke hana gudanar da aikin Hajji cikin nasara a duk shekara daga Najeriya ita ce, gwamnatoci ba su nada jami’an alhazai nagari. “Saboda haka akwai bukatar gwamnatoci su rika zabar mutane masu jin tsoron Allah da tausayi a matsayin jami’an alhazai, ta haka sai a rika samun nasarar yin aikin Hajji a Najeriya,” inji shi.
Ya nuna takaicinsa kan yadda jami’an alhazai a Najeriya suke yin watsi da alhazai a kasa Mai tsarki ba tare da suna tsayawa wajen sauke nauyin da aka dora musu na kula da su ba.
Ya shawarci gwamnatocin kasar nan su rika cire siyasa wajen nada jami’an alhazai, maimakon haka a rika nada mutane masu gaskiya da rikon amana. Ya ce muddin aka yi haka, Allah zai taimaka wa alhazan Najeriya su daina fuskantar matsaloli a yayin aikin Hajji.