A dade ana yi sai gaskiya

Bisa ga dukkan alamu dai rikicin da wasu gagga-gaggan ’ya’yan jam’iyyar APC da ke Majalisar Dattijai da ta Wakilai, a kardashin jagorancin Sanata Bukola Saraki, ya ki ci, ya ki cinyewa tun daga ranar da suka yi gaban-kansu wajen zaben kansu da kansu, da kuma biye ma zukatansu wajen nannada wasu manyan shugabannin majalisun guda […]

A dade ana yi sai gaskiya
A dade ana yi sai gaskiya

Bisa ga dukkan alamu dai rikicin da wasu gagga-gaggan ’ya’yan jam’iyyar APC da ke Majalisar Dattijai da ta Wakilai, a kardashin jagorancin Sanata Bukola Saraki, ya ki ci, ya ki cinyewa tun daga ranar da suka yi gaban-kansu wajen zaben kansu da kansu, da kuma biye ma zukatansu wajen nannada wasu manyan shugabannin majalisun guda biyu ba tare da amincewar jam’iyyarsu ba, da kuma kin bin umurninta wajen tabbatar da wadanda ta rigaya ta gabatar masu da sunayensu.

Wadannan al’amurra guda biyu sun tayar da kura ainun, sun kuma gawurta, har suna neman su buwayi uwar jam’iyya.
Hausawa dai sun ce dan da ya ce uwarsa ba za ta yi barci ba, shi ma ko runtsawa ba zai yi ba. Sanata Bukola ya hadiyi tabarya, haka nan zai tabbata a tsaye, ba daman zama ko kwanciya, har sai abin da hali ya yi nan gaba. Shi da shugabannin jam’iyyarsa sun sanya wando kafa guda domin kuwa sun fahimci cewa kokari yake ya kwashe gari bayan sun gama nika. Shi kuma abokin adawarsa na Majalisar Wakilai, Honorabul Yakubu Dogara, ya zare zare, ya bar ‘yan jam’iyyarsa da masilla a hannu, kuma a ganinsu abin da suka aikata zai dore har abada domin suna da dan karen wayon siyasa, amma abin da suka kasa fahimta shi ne shi dai tsuntsu mai wayo a wuya tarko ke kama shi, babu kuma yadda zai yi ya kubuta.
Shi ya sa ake ganin cewa idan sun san wata, ai ba su san wata ba. Tun da suka nuna tsananin taurin kai da rashin ladabi da biyayya ga jam’iyyar da suka bi ta kanta, suka kai ga zamantowa wakilai a majalisun nan guda biyu, ai tana iya yi masu doron mage, su kuma subuto daga bisa kololuwar da suka kai kawunansu ba da izninta ba. A halin yanzu idan hankulan wadancan shugabannin majalisun sun kai dubu a tashe suke, domin kuwa sun fahimci cewa jam’iyya dai ba ta tare da su, Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai ra’ayinsu, jama’an kasa kuma sun dawo daga rakiyarsu domin sun fahimci cewa a shirye suke su yi masu salalar tsiya, su wargaza tsarin da ake yi na tabbatar da samuwar canjin da talakawa suka yi amanna da shi a matsayin ceton da suka dade da sa ran zuwansa daga bakar ukubar da suka shekara 16 suna dandanawa a karkashin gwamnatocin PDP. Baicin haka nan kuma sun tabbatar da cewa babu abin da zai hana wadancan shugabannin biyu hada kai da baki da jam’iyyar PDP don yi wa jami’iyyar APC zagon kasa, daga karshe ma suna iya kyankyashe wata munakisa don tsige Shugaba Muhammadu Buhari.
To a yanzu jam’iyyar APC ta fahimci matsayar su Saraki, ta kuma dauki matakan ganin cewa ko ana ha-maza-ha-mata sai an canja wancan yanayin da suka dabbaka a cikin Majalisar Dattijai, ba kuma za su amince da ungulu-da-kan-zabon da aka samar a tsarin shugabancin majalisar dattijai ba, ganin cewa shi wancan sabon Mataimakin Shugaban majalisar Dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, mutum ne wanda idan ya samu rana zai yi shanya a cikin majalisar, kuma ko bayan faduwar ranar ba zai kwashe shanyar ba sai can da tsakar dare. A matsayinsa na mataimakin shugaba yana iya dana kujerar shugabanci, ya kuma jagoranci zaman majalisar, dangane da haka nan yana iya dakile duk wani yunkuri da dattijan majalisar za su iya yi don inganta manufofin jam’iyar APC a lokutan muhawara. Bar ta wannan! Ike Ekweremadu, a matsayinsa na mataimakin shugaba, shi ne shugaban kwamitin majalisar dattijai na yin gyararraki ga kundin tsarin mulki, kuma hakan zai ba shi daman dakile duk wani yunkurin da jam’iyyar APC za ta iya yi don yin gare-gare ga kundin tsarin mulki idan har hakan ba zai yi wa jam’iyyar PDP dadi ba.
Wadannan kadan ne daga cikin dalilan da ya sa jam’iyyar APC ke hankoron ganin an warware zabensa, an zabi daya daga cikin ’ya’yanta wanda zai kara tabbatar da cewa majalisar dattijan na biyewa da kuma marawa manufofinta a dukkan lokuta, tana kuma bayar da daman amincewa da dukkan shawarwari da dokokin da za a gabatar a majalisar. A matsayinta na jam’iyya mai rinjaye babu wani dalilin da zai sa jam’iyyar APC ta koma tamkar ’yar adawa a cikin majalisun biyu, ko kuma a dukkan lokuta da Shugaban kasa ya aike da wasu bukatu sai ta rage murya, tana neman alfarmar da za a muzanta kafin a yi mata, ko kuma ma a ki yi dungurungun.
To amma sai dai an ce ruwa bai tsami banza, sai da dalili, kuma idan ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa to ya taka dutse ne. Haka nan dai kawai banza ba ta kai zomo kasuwa, sai idan akwai wani abin da ya kai shi. Shi ya sa ake ganin cewa Sanata Bukola da Honorabul Dogara na da iyayen gidan da suke yi musu ingiza mai kantu ruwa, musamman ma wadanda suka lashi takobin taka wa Shugaba Buhari burki don kada binciken da zai yi ya yi tasiri ko wani armashi. Ko a waccan majalisar da ta gabata Sanata Bukola dai na daga cikin wakilan kwamitin binciken badakalar rarar farashin man fetur, kuma a halin yanzu ana zargin cewa wadanda ke ruwa da tsaki ne cikin waccan cuwa-cuwar, suka daure masa gindi, kuma idan bincike ya tsananta za a gano cewa da hannayensu dumu-dumu cikin kazantar da ke tattare da tallabin farashin man fetur din. Dangane da haka ne suka taru, suka cicciba shi hayewa mukamin da zai taimaka wajen hargitsa lissafi idan an nemi kawo wata dokar da za ta shafi haka a majalisa.
Yanzu dai a jira a ga yadda waccan dambarwar da ake fafatawa a majalisun kasa za ta kaya, domin kuwa an rigaya an ja daga tsakanin jam’iyya da fandararrun ’ya’yanta, kuma a irin wannan halin gaskiya ce kawai ke yin halinta, kuma ko ba dade, ko ba jima, gaskiyar za ta bayyana.