‘A daina amfanin da batun jirgin Oritsejafor ana bata kungiyar CAN’

Shugaban kungiyar Matasan CAN reshen Arewa ta Tsakiya, Injiniya Daniel KadzanYa bukaci masu amfani da batun jirgin saman Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Fasto Ayo Oritsejafor da aka kama a kasar Afirka ta Kudu wajen bata sunan CAN da shugabanninta su guji yin hakaInjiniya Daniel Kadzan ya bayyana haka ne a lokacin da yake […]

‘A daina amfanin da batun jirgin Oritsejafor ana bata kungiyar CAN’
‘A daina amfanin da batun jirgin Oritsejafor ana bata kungiyar CAN’

Shugaban kungiyar Matasan CAN reshen Arewa ta Tsakiya, Injiniya Daniel Kadzan
Ya bukaci masu amfani da batun jirgin saman Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Fasto Ayo Oritsejafor da aka kama a kasar Afirka ta Kudu wajen bata sunan CAN da shugabanninta su guji yin haka
Injiniya Daniel Kadzan ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Lafiya, inda ya ce abin mamaki ne yadda wasu mutane kamar su Malam Nasir El-Rufa’i da Sanata Geoge Akume ke sakin baki kan batun jirgin.
Ya kuma gargadi Jam’iyyar APC kan ta daina tsoma baki a cikin batun, maimakon haka ta mayar da hankali wajen kirkiro da dabarun da za su ba ta damar samun nasara a zabubbuka masu zuwa.
Ya ce Gwamatin Tarayya ta amince cewa ta yi hayar jirgin ne kuma kudinta ne da ta ware don sayo makamai don shawo kan ’yan ta’adda a kasar nan musamman a Arewa maso Gabas inda ’yan Boko Haram ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma. Amma duk da haka ’yan adawa sun ki barin Fasto Ayo ya huta don kawai an yi amfani da jirginsa.
Injiniya Kadzan ya gargadi cocin Katolika dya daina kirarin cewa a gudanar da bincike mai zurfi a kan batun inda ya ce kowa ya san Fasto Ayo a matsayin mutum da ke kai-kawo a kowane lokaci don tabbatar da an samu zaman lafiya a kasar nan baki daya. Ya ce maimakon cocin Katolika ya rika neman alfarma gun wata kungiya ko addini ya zo ya hada hannu da CAN wajen daukaka aikin Allah.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi