A daina danganta Fulani da kashe-kashen da ake yi a Najeriya – Ardo Ahmad
Ardo Ahmad Sulaiman shi ne Shugaban kungiyar Miyatti Allah na Kaduna, a zantawarsa da manema Labarai ciki har da Aminiya ya nuna rashin jin dadinsu a kan yadda ake zargin Fulani a duk lokacin da aka kai hare-hare a wasu yankunan kasar nan: Mene ne korafinku a kan zancen harin Kudancin Kaduna da kungiyar SUKAPU […]
Ardo Ahmad Sulaiman shi ne Shugaban kungiyar Miyatti Allah na Kaduna, a zantawarsa da manema Labarai ciki har da Aminiya ya nuna rashin jin dadinsu a kan yadda ake zargin Fulani a duk lokacin da aka kai hare-hare a wasu yankunan kasar nan:
Mene ne korafinku a kan zancen harin Kudancin Kaduna da kungiyar SUKAPU suke cewa mutanenku ke yi?
Wadannan kashe-kashe da ake yi gaskiya yana damun kowa a kasar nan. Sai dai abin da shugaban SUKAPU ya fadi cewa Fulani ne suka kai wannan hari gaskiya ba a yi wa Fulani adalci ba. Domin a wannan yanki babu Fulani bare kuma har su kai hari. Saboda haka bai kamata abubuwan da ake yi a Najeriya a danganta da al’ummar Fulani ba, idan an yi haka ba a yi wa Fulani adalci ba. Domin abin nan da muke ciki na kasar nan ko’ina wurare dai-dai ne babu irin wadannan hare-hare. Gaskiya duk inda aka je aka kashe mutane babu wani mai imani da zai ji dadi. Amma kuma bai kamata a danganta da wata kabila ba, saboda haka gaskiya ba mu ji dadi ba.
Ya kamata SUKAPU idan za su yi magana su rika fahimtar irin maganar da suke yi, wanda duk ya zama shugaban al’umma ya kamata idan zai yi magana ya yi magana mai kyau, ba wadda za ta harzuka mutane ba.
Abin da suke cewa shi ne a lokacin da aka kai harin akwai wani yaron da aka kashe wanda suka fahince Bafulatani ne kuma a wannan yanki yake?
In wannan yaron Bafulatani ne me ya sa aka kashe shi, su bar shi mana su kai shi gaban hukuma ya tabbatar daga inda ya fito kuma a tabbatar Bafulatani ne. Yanzu abin da mutane suka dauka shi ne da zarar sun ga farin mutum sai a ce Bafulatani ne, koda ba Bafulatani ba ne. Mu ba mu ji labarin inda aka kashe wani Bafulatani ba, saboda haka kuma wannan da aka ce Bafulatani ne ba mu yarda da hakan ba. Da yaron yana da rai an kawo shi a gabanmu a gaban kuma al’umma ya ce shi Bafulatani ne dole mu yarda, amma an rigaya an kashe shi saboda haka kowane ne ma sai a ce Bafulatani ne.
Yaya kuke ganin irin wadannan hare-hare da ake kaiwa Kudancin Kaduna da wanda aka kai Faskari a Jihar Katsina?
Wadanna hare-hare da aka kai a Kudancin Kaduna da Katsina abu ne da ba ya da dadin ji, halin da ake ciki yanzu a kasar nan abin da za mu ce Allah Ya sauwake. Su Fulani kansu kullum kai musu hari ake yi, ana kashe su ana kwace musu dukiyarsu. Saboda haka da wani dalili za a ce daon an kai wa wasu hari sai a ce wai Fulani ne. Su duk abin da ake yi musu ba su ce wai iri kaza ba ne ke kai musu hari sai wanda suka kama, wanda suka kama ne kawai za su ce wane ne. A yanzu babu wanda aka bari a kasar nan, mu muna rokon cewa in dai ba an ga tabbas ba a daina cewa Fulani ne suke kai wadannan hare-hare.
Akwai wanda ya bayyana a kafafen watsa labarai yana cewa shi Bafulatani ne kuma su suke kai wadannan hare-hare, me za ka ce?
Wannan ai irin mutanen nan ne mahaya, ya ce shi Bafulatani ne amma da za a bincika ba Bafulatani ba ne, ya fadi maganar ne saboda ya bata sunan Fulani ko saboda yana da wata bukata ko manufa. Saboda son bata wata al’umma kana iya fadin ko ma mene ne, amma in abu ya tabbata a yi shi a zahiri hukuma ta sani, mutane su sani ’yan jarida su sani shi ne bayani.
A ina Fulani suke gudun hijira a Kaduna yanzu?
Gaskiya a sakamakon abin da ya auku a Kudancin Kaduna akwai Fulani da yawa da suka watsu a wasu wurare. Misali akwai su a Lere da Zangon Kataf da Mariri zuwa har inda ake cewa Ramin Kura. Duk in ka je al’ummar Fulani ne za ka gani kuma suna nan a watse. Wasu ma sun tashi daga can zuwa Benuwai saboda Bafulatani shi bai iya zama wuri daya ya ce wai yana jira a kai masa gudunmawa. Bafulatani bai iya haka ba, kamar yadda idan abu ya samu wasu kabilu za su hadu a wuri daya suna jiran gwamnati ta kai musu tallafi, su Fulani duk rikice-rikicen da aka yi tun daga shekarar 2011 har zuwa lokacin nan duk suna watse ba su taba samun taimako daga Hukumar Bada Tallafin Gaggawa ta SEMA ko NEMA, tunda ba su saba da zama wuri daya ba da yaro da uwa da uba su hadu a daki daya ba, Bafulatani bai iyawa. Idan kuma sun watse babu wanda yake bin su, sai dai mu shugabaninsu mu bi su mu ba su hakuri in akwai abin da Allah Ya hore a yi in kuma babu a ba su hakuri mu ce Allah Ya sauwaka.
Yaya zancen satar shanu da ake yi muku?
Maganar sace-sacen shanu ko kwannan nan akwai wanda ya zo ya same ni a gida ya ce an kora masa saniya 250, akwai kuma wanda ya ce an kora musu garke shida a yamma da Zariya inda ake cewa Karau-Karau. Kuma akwai dan uwana da aka kora wa 70. Mu dai a kan wannan magana babu abin da zamu ce sai Allah Ya sauwake domin abin ya wuce misali.
Masu satar nan ana danganta su da cewa su ma Fulani ne, haka ne?
Abin da ya sa ake cewa Fulani shi ne, da an ga mutum siriri mara jiki kuma fari sai a ce ai Bafulatani ne. Kuma kila wanda duk ya bi daji yana kashe mutane kila sirri ne fari saboda haka in ma akwai Fulani batagari mu dai wadanda muke kamawa babu yaren da ba mu kama ba.
Ko ranar Juma’ar nan mun kama Fulani 77 a nan Marmara. Shanun na wani Kanar ne a soja. Muna kamawa kuma wasu ba sa jin Hausa, saboda haka abu na sata mu tunda muke a duniya ba mu taba ganin irin yadda ake wannan sata ba.
Kuma mun tabbatar tare da yin imani da Allah masu korar shanun nan akwai baki kuma sun hada kungiya ce.