A daina dora wa APC laifi kan matsalolin Najeriya – Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai Barista Yakubu Dogara ya bukaci masu sukar gwamnatin Jam’iyyar APC su daina dora wa gwamnatin APC din laifi kan matsalar tattalin arziki da Najeriya ke ciki a yanzu.Shugaban Majalisar Wakilan ya yi kiran ne cikin wata sanarwa da Mashawarcinsa na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Hulda da Jama’a, Turaki Hassan ya […]

A daina dora wa APC laifi kan matsalolin Najeriya – Dogara
A daina dora wa APC laifi kan matsalolin Najeriya – Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai Barista Yakubu Dogara ya bukaci masu sukar gwamnatin Jam’iyyar APC su daina dora wa gwamnatin APC din laifi kan matsalar tattalin arziki da Najeriya ke ciki a yanzu.
Shugaban Majalisar Wakilan ya yi kiran ne cikin wata sanarwa da Mashawarcinsa na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Hulda da Jama’a, Turaki Hassan ya fitar a ranar Talatar da ta gabata a Abuja.
Sanarwar ta ce Barista Dogara ya bayyana haka ne a lokacin da ya karvi bakuncin injiniyoyi da direbobin jiragen sama da gwamnatin Jihar Bauchi ta dauki nauyin karatunsa da ba su fara aiki ba, wadanda suka kai masa ziyarar girmamawa a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talata.   
Ya ce maimakon a dora wa gwamnatin APC laifi, kamata ya yi a zargi mutanen da suka jefa Najeriya a halin da take ciki a yanzu.
Barista Yakubu Dogara ya ce gwamnatin Shugaban Buhari tana yin aiki wurjanjan wajen gyara al’amuran kasar nan kuma za a dauki wani lokaci kafin a cimma nasarar haka.
“Kun san kalubalen da muke fuskanta a kasar nan a halin yanzu. Duk da cewa mutane ba su son yin magana kan abin da muka yi kamfe a kai cewa za mu gyara kasar nan. Mun shuka abin da muka shuka, kuma yanzu muna girbar abin da muka shuka ne, sannan abu ne sananne cewa akwai lokacin shuka, akwai kuma lokacin girbi. Don haka ba za mu so mu yi ta magana kan abin da ya faru a baya kawai ba, muna fuskantar gaba ne,” inji shi.
Shugaban Majalisar ya bukaci matasa marasa ayyukan yi a kasar nan da kada su yanke kauna, inda ya ba su tabbacin cewa gwamnati tana yin duk abin da ya wajaba wajen kirkiro da hanyoyin samar da ayyukan yi.
“Zuba kudi a vangaren ilimi da koyar da sana’a da karatu ba asara ba ne,” inji shi. Kuma ya ce yana da yakini gwamnati za ta rage rashin aikin yi a kasar nan.
“Kada ku yanke kauna, domin babu wani ilimi ko horo da ke zama banza; kuma nauyi ne a kanmu mu bude kofofi ga kamfanoni masu zaman kansu domin su samar da aikin yi,” inji shi.
Ya bukaci ’yan Najeriya su hada hannu da gwamnati wajen gyaran kasar nan tare da samar da ayyukan yi musamman ga matasa. “Idan ba a samar da aikin yi ga matasa ba, zai zamo illa ga al’umma, tare da kashe gwiwar wadanda ake yayewa daga makarantu,” inji Dogara.
Tun farko a jawabin jagoran ayarin, Kyaftin Bala Jibrin, ya ce direbobin jiragen saman da injiniyoyinsu, gwamnatin Jihar Bauchi ce ta dauki nauyin karatunsa zuwa kasar Amurka, kuma sun kammala karatun a shekarar 2011.