A daina jifar ma’aikatanmu lokacin da suka fita kashe gobara – Manzo
Babban Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Gombe Mista Kudiri Manzo, ya nuna takaicinsa kan yadda wasu jama’a ke jifar ma’aikatansu a lokacin da suka je kashe gobara.Mista Kudiri Manzo, ya bayyana wa wakilinmu cewa aikinsu na kashe gobara aiki ne na ceto rayuka da dukiyoyin al’umma daga halaka kuma a duk lokacin da aka […]
Babban Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Gombe Mista Kudiri Manzo, ya nuna takaicinsa kan yadda wasu jama’a ke jifar ma’aikatansu a lokacin da suka je kashe gobara.
Mista Kudiri Manzo, ya bayyana wa wakilinmu cewa aikinsu na kashe gobara aiki ne na ceto rayuka da dukiyoyin al’umma daga halaka kuma a duk lokacin da aka kira su suna zuwa ba bata lokaci kuma ba a biyansu kudi idan suka kashe gobarar. Ya ce rashin fahimta ne wasu mutane musamman matasa idan ma’aikatansa suka fita kashe gobara a rika jifar su.
Ya ce da mutane sun san yadda aikinsu yake da ba za a rika jifar su ba, ya ce a mafi yawancin lokaci masu jifan nasu barayi ne da ba sa son a kashe wutar da wuri saboda suna yi wa jama’a sata.
Mista Manzo, ya ce wani lokacin idan suka fita kashe gobarar irin wadannan batagari sukan karbe tiyo din a hannunsu suna zubar da ruwan a gefe don kada wutar ta mutu da wuri wasu kuma suna sata a gefe.
Ya ce suna bukatar karin ma’aikata sosai domin duk fadin Jihar Gombe ma’aikatansu 82 ne kuma akalla ya kamata a ce sun kai 200 zuwa 300.
Babbban Daraktan ya ce kuma galibin ma’aikatansu za su isa yin ritaya nan da shekara biyar masu zuwa, kuma idan suka yi ritaya babu wadanda za su koya wa na bayan aikin ke nan.
Mista Manzo, ya ce daga watan Janairu zuwa Yulin bana, sun ceto rayuka 1,813 yayin da aka samu asarar rayukan mutum 17 tare da salwantar dukiya ta sama da Naira miliyan 28 da dubu 469 dari da 200, yayin da suka ceto kayayyakin da suka kai na Naira biliyan biyu da miliyan 533 da dubu 144 da Naira 100 a gobara daban-daban da suka kai dauki.
Ya ce karancin kayan aiki ne da yadda mutanen gari ba su cika ba su hadin kai ya sa asarar ta yi yawa.
Ya ce batun cewa suna zuwa kashe gobara ba su da ruwa ba gaskiya ba ne, ya ce motar tasu ba ta wuce durom 10 zuwa 15, kuma idan suka bude ruwan da karfi sai ya kare da wuri saboda tiyo dinsu yana zubar da lita 25 na ruwa a cikin dakika daya.