A daina jingina wa Musulunci munanan abubuwa – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya shawarci ’yan Najeriya su daina jingina wa Musulunci munanan abubuwa a kasar nan, inda ya ce babu wata kasa da za ta iya shanye yakin addini.Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen buda baki da ya shirya wa malamai da […]

A daina jingina wa Musulunci munanan abubuwa – Sarkin Musulmi
A daina jingina wa Musulunci munanan abubuwa – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya shawarci ’yan Najeriya su daina jingina wa Musulunci munanan abubuwa a kasar nan, inda ya ce babu wata kasa da za ta iya shanye yakin addini.
Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen buda baki da ya shirya wa malamai da jami’an tsaro da shugabannin al’umma da manema labarai da shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu da sauransu a fadarsa, inda ya ce ana tauye Musulmi a kasar nan, sai dai kawai ba su yin korafi ne.
 “Idan aka nada Bahaushe a kan wata kujerar mulki sai mu kira haka fifita ’yan Arewa, kuma idan Shugaba Musulmi ya ziyarci wata kasar Musulunci sai mu ce yana kokarin musuluntar da Najeriya ne, alhali akwai mutane da dama daga sauran addinai da kabilu da suke rike da mukaman shugabanci kuma mun sha ganin shugabanni Kiristoci da dama suna ziyartar kasashen Kirista amma babu wanda ya ce suna kokarin Kiristansar da kasar nan,” inji Sarkin Musulmi.
Sarkin Musulmin ya ce ana sanya siyasa a cikin komai, duk wani mummunan abu sai a jingina shi da Musulmi ko Fulani (makiyaya) ko Hausawa, alhali sauran mutanen da suke aikata miyagun ayyuka a sauran wurare ba a jingina su da addininsu ko kabilarsu ko yankinsu.
 Ya ce Najeriya kasa ce mai kyau da talakawanta suke kaunar juna, sai ya dora alhakin matsalolin da kasar take cike kan ’yan boko da shugabanni. Ya ce ’yan boko da shugabannin ne manyan matsalolin kasar nan, saboda halayensu na son kai da rashin hakuri, inda ya ce: “Duk lokacin da wani ya rasa mulki sai ya jawo matsala, kuma talakawa ne suke dandana kudarsu.”
Ya nuna mamaki kan yadda mutane suke dora laifin duk wani hari da aka kai a kan Fulani, inda ya ce “Idan miyagu suna yin munanan abubuwa su miyagu ne kuma ana iya samunsu a ko’ina, a cikin kowane addini ko kabila ana iya samun masu aikata ta’addanci.”
Da yake tofa albarkacin bakinsa wani limamin addinin Kirista da ke zaune a Kaduna Fasto Yohanna Buru ya roki Musulmi da Kirista su rika yafe wa juna a duk lokacin da suka musguna musu.

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

Iran da Amurka sun daidaita tattaunawar sulhu a Switzerland