A daina kiranmu ’yan Boko Haram

Ranar Talata, mutanen Arewa mazauna Jihar Abiya suka bukaci Gwamna Theodore Orji ya taimaka a daina kira kowanensu dan Boko Haram, musamman ma ganin cewa babu wanda ke goyon bayan ’yan Boko Haram din daga Arewa.Haka nan sun bukaci Gwamnan da kuma hukumomin tsaro su ja wa wani Pasto Jubril John birki, wanda yakan zagaya […]

A daina kiranmu ’yan Boko Haram
A daina kiranmu ’yan Boko Haram

Ranar Talata, mutanen Arewa mazauna Jihar Abiya suka bukaci Gwamna Theodore Orji ya taimaka a daina kira kowanensu dan Boko Haram, musamman ma ganin cewa babu wanda ke goyon bayan ’yan Boko Haram din daga Arewa.
Haka nan sun bukaci Gwamnan da kuma hukumomin tsaro su ja wa wani Pasto Jubril John birki, wanda yakan zagaya yana sukar Musulunci kuma yana zuga Ibo su kyari al’ummar Arewa, lamarin da, in ba a ja masa birki ba, yana iya haifar da tashin-tashina cikin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kiristoci da musulmin jihar.
Babban Limamin masallacin Juma’a na Aba, Alhaji Idris Bashir, wanda ya yi magana a madadin al’ummar Arewa, ya ce ya yi amanna cewa a matsayin Gwamna Orji na shugaban jiha, idan ya yi wa jama’a magana, za su saurare shi su daina bahaguwar dabi’ar da suke nuna wa makwabtansu musulmi.

Ya ce duk da kokarin da al’ummar Arewa suke yi na barrantar da kansu daga harkokin da ’yan Boko Haram ke yi, mutanen jihar sai kokarin hada su suke yi.
Alhaji Bashir ya ce ko kwanan nan sai da musulmi suka gudanar da wata zanga-zangar lumana ta kwanaki uku don nuna rashin amincewarsu kan danganta su da ake yi da Boko Haram din, sannan suka dakatar da ita saboda sa bakin da Kwamandan Sashe na ’yan sanda, kan lamarin. “Mun yi zanga-zangar ce don mu nuna cewa al’ummar musulmi suna alhini da yadda ake kallonsu da daukarsu a jihar ta Abiya”. Inji shi.
Ya ce akwai ’yan Arewa da dama da suke zaune a garin Aba tun kimanin shekaru sittin (60) da suka wuce kuma ba za a iya nuna wani halin wadarai da suka aikata ba, saboda haka ba daidai ba ne a kira kowane mutamin Arewa dan Boko Haram.
“Suna zagin mutanenmu a wurare kamar asibitin St. Paul da gefen dakin Taro na Aba da titin Azikiwe, wanda ya hadu da na Adazi da ma sauran wasu wurare. Kuma tun lokacin da sojoji suka kama ’yan Arewa 486 da suke kan hanyarsu zuwa sassan Kudu maso Gabas da Kudancin Kudu, wani pasto Jubril John, wanda yake magana da yarukan Najeriya da dama, ya kama yawon wa’azin nuna kiyayya, yana neman tunzura Ibo kiristoci a kan musulmi”. Inji shi.
Ya ce shugabannin Arewa da ke zaune a Aba za su kai kukan dabi’un Pasto Jubril John ga kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).  “Yadda lamarin yake shi ne shi wannan pasto yana jin Hausa da Ibo da Yarabanci sosai, kuma yana da littattafan Musulunci masu yawa, yana wa’azinsa cikin jama’a.  Yana zuwa kasuwar Ariara da titin Jubilee da Cameroon da duk wuraren da ya san akwai musulmi ya rika wa’azin sukar Musulunci”.  Inji shi.
Alhaji Bashir ya ce duk da ya je ya sadu da paston, ya nuna masa hadarin yanayin wa’azinsa, bai daina ba.  Ya sanar da ma’aikatan tsaro game da lamarin, amma har zuwa lokacin da yake magana da wakilinmu, ba a yi komai a kai ba.
Sai ya ja hankalin al’ummar musulmin Aba da su kasance natsattsu a kodayaushe da kokarin kyautata zaman lafiya duk da irin wannan kyara da ake musu.
kokarin wakilinmu ya ji ta bakin Jami’in hulda da jama’a na ’yan sanda Geoffrey Ogbonna ya ci tura, amma Sakataren labarai na gwamna, Mista Charles Ajunwa ya ce, “Babu wani abu da ya yi kama da haka a wurinmu”.