A daina sakaci da rikicin makiyaya da manoma –Sardaunan Katsina
Yallabe me ya sa ba a shirya hawan daba a Kaduna duk shekara ba sai idan wani abu ya taso? Idan aka tattauna gwamnonin Arewa da sarakunan Arewa suka ga ya kamata a rika yin duk shekara daidai ne. Kafin zaben shekarar 2015 na yi kokarin fadakar da mutanen Arewa cewa a 1959 muka samu […]

Yallabe me ya sa ba a shirya hawan daba a Kaduna duk shekara ba sai idan wani abu ya taso?
Idan aka tattauna gwamnonin Arewa da sarakunan Arewa suka ga ya kamata a rika yin duk shekara daidai ne. Kafin zaben shekarar 2015 na yi kokarin fadakar da mutanen Arewa cewa a 1959 muka samu ’yancin kanmu saboda haka muka shirya bikin wayar da kai domin tuna ranar 15 ga Maris 1959. Abin da muke so shi ne a hada kai, duk rikice-rikicen da ake samu, da rashin yarda da juna mu a ACF mun shirya taron wayar da kai mai taken zaman lafiya da hadin kai da ci gaba.
Idan Arewa ta hada kanta, ta rage rikice-rikice, ta zauna lafiya sai mu kawo abubuwan gaba. Amma kullum abubuwan sai dada lalacewa suke yi. Kudu mun san yadda muke da su, abin da ya faru a Taron kasa na shekarar 2014, ya kamata ya fadakar da mu mu zauna lafiya mu girmama juna kamar yadda Allah Ya hada mu.
Mun taba samun shugaban da ya hada kan ’yan Arewa wato Sardauna Sa Ahmadu Bello yana mulki babu inda ba taka ba domin nemo hadin kan Arewa. A mota ce a kwale-kwale da jirgin sama ne, muna da fina-finan abubuwan da ya yi.
Yanzu muna da jihohi 19 kuna taro, yanzu Gwamnan Borno ne shugabansu. Akwai kungiyoyi irin su ACF da dukansu ’yan Arewa ne suka kafa, akwai Cibiyar Tunawa da Ahmadu Belllo gwamnonin ne suka ba da karfi aka kafa ta. Me ya sa ba za mu rika amfani da wadannan abubuwa domin gano matsalarmu da abin da ya kamata mu yi ba? Ga sarakuna da sauransu sai a zauna a tantace a ce ga abin da ya kamata a yi.
Kullum kirana hadin kanmu, idan muka bari za a lalata mu domin kullum ana cewa ba a sonmu don haka ya kamata mu wuce inda muke a yanzu.
Shugaban kasa Buhari ya bai wa Shugaban ’Yan sanda umarnin tarewa a Jihar Benuwai. A matsayinka na masanin tsaro ta yaya za a magance rikicin yankin?
Me ya kawo rikice-rikice a can? Ba an yi doka ba, shin ya dace a yi dokar? Jihar Taraba ta yi, Benuwai sun yi to, me ake nufi? Kada ka manta da batun Arewa ta Tsakiya, su ukun suna cikinta. A shekarar 2015 mun yi ta kokarin hada kan kowa amma da aka yi zaben shekarar 2015 su wa suka zabi Buhari, ’yan Arewa ciki har da Filato da Benuwai da Taraba.
Kudu maso Yamma sun raba kafa kowa ya ci za su ce ai sun taimaka masa. Kudu maso Gabas sun zabe mu? Kudu maso Kudu sun zabe mu? Kano su suka bayar da mafi rinjiyen kuri’a, sai Arewa maso Yamma da sauransu. A takaice Arewa ce ta zabi Shugaba Buhari. Amma abubuwan da ya kamata a samu na ci gaba mun same su?
Batun fadada Kogin Baro a Lakwaja an gama? Kun san amfaninsa, kudin ma da aka ware a baya, karkatar da shi aka shi zuwa yankin Neja-Delta. To, irin wadannan abubuwa muke so a yanzu a fiddo mana da hakkinmu.
Game da rikicin Fulani makiyaya da sauran kabilu manoma, mafita ita ce a bincika a gano mene ne gaskiyar batun. Kai ka san gaskiyar yanzu? Da ana zaune lafiya tun ba ma can Benuwai ba, an ce zaman lafiya ake yi sosai da Tibi da Fulani har suka zo suna cinye musu shanu sai aka sa musu suna ‘Munci’ mun cinye har ya zo ana wasa da su.
Joseph Tarka ne shugabansu daga baya ba ya dawo ya zama abokin Sardauna. Aminu Kano NEPU yake yi amma idan sun shiga daki hada kai suke yi da Sardauna domin kare martabar Arewa. Amma yanzu me yake samunmu, laifinmu ne duk ’yan Arewa da manyan da matasan ya kamata mu hada kanmu. Rayuwar ’ya’yanmu da jikoki muke neman karewa. Mu yi tunani rikicin Fulani makiyaya da manoma babbar matsala ce, kada a yi sake ko kadan. Muna yin kokarinmu wajen samu bayanai da yin kiddiga kafin mu fitar da maslaha ta bangarenmu.
Wane kira kake da shi ga shugabannin Arewa?
Abubuwa sun lalace sun tabarbare kowa ya san gidansu. Komai kake takama da shi ka san inda ka fito. Daga nan Allah Ya daga ni na zama Shugaban ’Yan sandan kasa. Kuma ga shi na dawo, ban je na zauna a Legas ko Abuja ko Kano kamar yadda wadansu ke yi ba. To, in ba mu da kishi ba za mu je ko’ina ba. Sai kuma tsoron Allah da adalci in ba mu da wadannan ba za mu je ko’ina ba.
Ina ASP aka kai ni Legas aiki lokacin abin da suke cewa Malam ya iso. Suna nufin masu gaskiya sun iso, amma daga baya ai barayi suke ce mana, in da mun ci gaba da yadda muka faro da ba haka ba.
Lokacin da ’yan Kudu suke son a ba da ’yancin kai a 1956, ai Sardauna cewa ya yi a’a sai mutanensa sun dago a fagen ilimi da sauransu, a 1957 ne yankunan Yamma da Gabas suka samu ’yancin kai, mu kuma sai a 1959. Ka duba daga 1956 zuwa 1959 har 1960 mun taso saboda gaskiya da shirya kwasa-kwasai da sauransu, daga nan muka fara karbar mukamai. A lokacin idan mun je Legas abin sha’awa muke, saboda gaskiya amma daga baya fa?
Aikin dan sanda ba ni na ce ina so ba, sanya ni aka yi saboda kishin Arewa, Sardauna a lokacin idan ya samu labarin za a dauki aiki a Gwamnatin Tarayya zai tabbatar da kashi 50 ’yan Arewa ne kashi 50 kuma ’yan Kudu, saboda adalci.
Ni ne Shugaban ’Yan sanda na biyu mafi ddewa a kan mukamin, na farko Alhaji Kam-Salem wanda ya yi shekara tara, ni kuma shekara shida. Na fara da Janar Babangida sai Shonekan, sai Janar Abacha da Janar Abdulsalami wanda ya mika mulki kasa da shekara daya, shi ya sa ake girmama shi a duniya.
Mun mika mulki ga Obasanjo shi kuma maganarsa daban ce domin ko shi ya san na yi ta magana a kansa. Mu ’yan Arewa ne kuma muna da makiya masu so su ga sun mallake mu kuma yanzu mun yar da kishi ba mu yin tunanin yadda za mu hana su.
Su wane ne ’yan Boko Haram ai akwai gwamnati da ta yi mulki shekara shida me ta yi wajen magance matsalar? Kudin da aka ce an ware wajen samar da tsaro me aka yi da su? Lokacin Buhari an fiddo su to, me aka yi da su? Ba an zo an kori wadansu masu shari’a ba, kuma sun dawo, me aka yi? An ce canji-canji har aka samu canji na gwamnati to, me aka yi? Mu rika tunani tare da yin bincike. Gwamnatin Buhari ta bai wa mutumin Legas manyan ma’aikatu biyu.