A daina sayen hauren-giwa- Inji Jackie Chan

Jarumi Jackie Chan ya bukaci masu sayen  hauren-giwa da fatun damusa da sauran dabbobin da ke barazanar bacewa a doron kasa da su  daina.Jarumin ya yi kiran ne a Birnin Landan inda ake gudanar da wani babban taron da ya samu halarta kasashe fiye da 40. Makasudin taron dai shi ne a kawo karshen farautar […]

A daina sayen hauren-giwa- Inji Jackie Chan

Jarumi Jackie Chan ya bukaci masu sayen  hauren-giwa da fatun damusa da sauran dabbobin da ke barazanar bacewa a doron kasa da su  daina.
Jarumin ya yi kiran ne a Birnin Landan inda ake gudanar da wani babban taron da ya samu halarta kasashe fiye da 40.
Makasudin taron dai shi ne a kawo karshen farautar dabbobi da ake yi ba bisa ka’ida ba don dakile barazanar bacewarsu daga doron kasa.
Galibi dai akan yi farautar namun daji kamar su: giwa da damusa da zaki da rakumin dawa da sauransu don sarrafa su zuwa kayayyakin amfanin yau da kullum. Misali ana amfani da hauren-giwa wajen yin abin wuya; fatun wasu dabbobin kuma akan yi takalma da jaka da bel da sauransu, inda ake amfani da wani bangare na jikin zaki don yin asiri.