A daina tsoma Masarautar Bauchi a cikin harkokin siyasa – Shehu Buba

Idan mai sarauta ya faɗi ra’ayinsa a siyasance bai kamata a ɗauki mataki a kansa ba.

A daina tsoma Masarautar Bauchi a cikin harkokin siyasa – Shehu Buba

Al’ummar Masarautar  Bauchi sun roki Gwamnatin Jihar Bauchi ta guji sanya Masarautar Bauchi a cikin harkokin siyasa don guje wa zubar da mutuncinta.

Wannan kiran ya biyo bayan warware sarautar Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu da masarautar ta yi ne bisa zargin rashin ladabi ga Gwamnan Sanata Bala Abdulkadir Mohammed.

Sanata Shehu Buba shi ne mutum na biyu da masarautar ta warware sarautarsa, bayan sauke tsohon Wazirin Bauchi, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, wanda hakan ya sa ake zargin shigar da harkokin siyasa a masarautar.

Hakazalika, masarautar ta dakatar da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara daga sarautarsa ta Jakadan Bauchi. Kuma ta dakatar da Alhaji Yakubu Shehu Abdullahi daga sarautarsa ta Wakilin Birni.

A martaninsu daban-daban, Alhaji Nasiru Ibrahim da Tijjani Mahmud Kolo da Muhammad Jibril Sogiji sun ce, ka’idodin siyasa daban na sarauta daban.

Sun ce a cikin harkokin siyasa akwai adawa mai ma’ana, wadda halattacciyar aba ce a siyasa da nufin sa gwamnatin da ke mulki ta kyautata wa al’ummarta.

“Saboda haka, idan mai rike da mukamin sarauta ya faɗi ra’ayinsa a siyasance bai kamata a tilasta wa masarauta ɗaukar mataki a kansa ba, ko ita kanta masarauta bai kamata ta ce don an yi zargi na siyasa ga gwamnatin da ke kan mulki, ta nuna ba ta ji daɗin abin ba, kuma a ce za a hukunta wanda ya yi hakan.

“Kamata ya yi a bar ’yan siyasa a tsakaninsu, sun fi masarauta sanin junansu a siyasance kuma za su warware matsalolinsu, amma shigar da masarauta ciki na jawo zubar da mutuncin sarauta,” in ji su.

Sanata Shehu Buba Umar shi ma ya mayar da martani bayan samun labarin warware naɗin sarautarsa ta Mujaddadin Bauchi.

Sanata Shehu Buba Umar ya ce, “Na samu labari mai cike da ban mamaki game da wasikar da ke ɗauke da kwanan wata 14 ga Agusta, inda aka sanar da ni cewa, Majalisar Masarautar Bauchi ta cire ni daga sarautar Mujaddadin Bauchi sakamakon zargin cewa na ci mutuncin Gwamnan Jihar Bauchi a wani gangamin yakin neman zaɓe.

“Ina amfani da wannan dama in sanar da cewa tun lokacin da na shiga siyasa ba na bin wani tsari face suka mai ma’ana, ba tare da cin mutunci ko zagi ba, kuma tsarin da nake bi tsari ne na nufin samar da ingantacciyar al’umma,” in ji Sanata.

Ya ce, “Lokacin da na saurari kalaman Gwamna Bala Mohammed a kan Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, sai na ga ya zama wajibi gare ni in kare Shugaban Ƙasa daga yunkurin da ake yi na ɓatawa da lalata kimarsa da sa kiyayyarsa a zukatan al’umma, wanda haka na yi a yakin neman zaɓen da Jam’iyyar APC ta yi da na halarta kwanan nan.

“Amma  maganganun  Gwamna Bala Mohammed a kan Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu da kafafen yaɗa labaran kasar nan da dama suka ruwaito sun kunshi fito-na-fito da zargi marar tushe da amfani da kalaman da ka iya kawo barazana ga tsaro a kasa.

“Kuma ina nanata cewa, zarge-zargen da Gwamna Bala Mohammed ya yi wa Shugaba Tinubu, kalamai ne na siyasa, kuma ba su da wata cikakkiyar hujja.

“Sannan a kalaman da na yi na musanta zargin da Gwamnan ya yi wa Gwamnatin Tinubu na rashin kula da aiki da kare hakkokin al’ummar kasa, amma na zargi Gwamna Bala da aikata hakan.

“Sannan na bayyana cewa, Gwamna Bala Mohammed ya karɓi Naira biliyan 144 daga Asusun Tarayya a 2023 da fiye da Naira biliyan 147 daga watan Janairu zuwa yau, wanda ake sa ran a jumlace kafin karshen shekara kuɗin da zai karɓa za su kai Naira biliyan 195, inda na nemi bahasi cewa me Gwamnatin Bala Mohammed ta yi da waɗannan kuɗaɗe, wanda ina ganin tambayar haka ba laifi ba ne.

“Haka na ce Gwamna Bala Mohammed ya ciwo bashin Naira biliyan 300, don haka ya faɗa wa al’ummar Jihar Bauchi me ya yi da waɗannan makudan kuɗaɗe da jihar ta karɓo sakamakon yadda al’umma ke kukan yunwa duk da cewa gwamnatin ta karɓi biliyoyin Naira daga Asusun Tarayya.

“Kuma Shugaban Ƙasa ya bai wa jihar hatsi tirela 70 da taki tirela 70 da shinkafa tirela 20 a raba wa mutane, me gwamnati ta yi da su?

“Duka waɗannan kalamai na yi su ne da kyayyakwar niyya da kuma kare shugabanci na sama ba na matakin jiha ba.

“Sannan ina mamaki da nadamar yadda Majalisar Masarautar Bauchi ta gaggauta yanke hukunci a kan kalamaina ba tare da ta ji ta bakina ba.

“Saboda haka matsayar da Masarautar Bauchi ta yanke a kaina na karɓa da kyakkyawar niyya, sannan ina sa ran cewa Allah zai aiko da wani maceci da zai zo ya ceci Jihar Bauchi daga halin da take ciki,” in ji shi.

Ya kara da cewa “Ina shawartar Majalisar Masarautar Bauchi ta guji waɗanda za su rika yin amfani da ita domin cim ma manufofinsu na son rai da kare muradun wasu.

“Sannan ina addu’a Allah Ya ja zamanin Mai martaba Sarkin Bauchi cikin koshin lafiya domin tafiyar da wannan masarauta.”

A halin da ake ciki al’ummar jihar na ci gaba da faɗin albarkacin bakinsu kan lamarin.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta