A daina yada labaran karya akan yin garkuwa da mutane – ‘Yan sanda

Hukumar ‘yan sandan jihar Enugu ta gargadi jama’ar jihar da su daina yada labaran karya a shafukan sada zumunta na zamani akan yin garkuwa da mutane a jihar. Jami’in hulda da jama’a na Hukumar ‘yan sandan jihar (PPRO) SP Ebere Amaraizu, ya sanar da gargadin a Enugu yau Talata. Amaraizu ya ce, a yanzu haka […]

A daina yada labaran karya akan yin garkuwa da mutane – ‘Yan sanda

Hukumar ‘yan sandan jihar Enugu ta gargadi jama’ar jihar da su daina yada labaran karya a shafukan sada zumunta na zamani akan yin garkuwa da mutane a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na Hukumar ‘yan sandan jihar (PPRO) SP Ebere Amaraizu, ya sanar da gargadin a Enugu yau Talata.

Amaraizu ya ce, a yanzu haka hukumar ‘yan sandan ta fara binciken labarun karya da ake yada wa tare da hadin gwiwar kamfanonin sadarwa don kama masu aikata wannan laifin.