A daina yi wa Fulani kudin goro —Gan Allah Fulbe

Shugaban Kungiyar Ci gaban Fulani ta Gan Allah Fulbe, Alhaji Sulaiman Yakubu, ya kira bugun kadanya da ake yi wa Fulani a sassan Kasar nan, musanmman ma a wasu jihohin Arewa maso Yammacin Kasar nan da suka hadar da Sakkwato da Zamfara da Kebbi. Ya ce, cin kashin da ake yi wa Fulanin a Arewa […]

A daina yi wa Fulani kudin goro —Gan Allah Fulbe

Matasan Fulani suna rawa a wajen bikin Ranar Fulani da aka gudanar a garin Wase lokacin nadin Bauran Wase

Shugaban Kungiyar Ci gaban Fulani ta Gan Allah Fulbe, Alhaji Sulaiman Yakubu, ya kira bugun kadanya da ake yi wa Fulani a sassan Kasar nan, musanmman ma a wasu jihohin Arewa maso Yammacin Kasar nan da suka hadar da Sakkwato da Zamfara da Kebbi.

Ya ce, cin kashin da ake yi wa Fulanin a Arewa ko a Kudancin Najeriya ya yi yawa.

Yakubu ya ce, ko a baya-bayan nan tafiya ta kama shi zuwa Jihar Sakkwato, inda suka iske wasu ’yan sa-kan sun tsare wasu matan Fulani bayan sun fito da su daga cikin motar da ke dauke da su.

“Ko da muka isa wajen sai na tsaya na tambayi matan daga ina suke su kai mana bayani suna kan hanyarsu ce ta zuwa Kaduna sun fada mana wajen wadanda za su je, nan muka shiga tsakani aka ba mu su muka tsallake da su, ba don Allah Ya kawo mu wajen ba, da kwanansu ya kare domin ’yan sa-kan za su hallaka su ne, don su aikinsu ke nan daga sun ga bafulatani namiji da mace sai su tare su kashe.

“Sau tari jami’an tsaro na yunkurin su hana su, amma sai su ki suna cewa jami’an tsaron na goyon bayan ’yan bindiga, su kuma jami’an tsaro suna da horo, kuma a karkashin dokar kasa suke aiki.

“Don haka, ba sa yin kisan gilla irin na ’yan iskan, domin su suna aikinsu ne da bincike, don haka muna kira ga mahukunta musamman gwamnati ta sanya ido a kan kisan da ’yan sa-kan ke yi wa Fulanin da ba su ji ba ba su gani ba, domin wannan abu shi ke kara rura wutar rikicin, don ba yadda za a yi a ce duk bafulani dan bindiga ne mai laifi, kamar yadda ba za a ce duk mutanen Maiduguri ko Jihar Barno ’yan Boko Haram ba ne, to haka su ma ba duk Fulani ne ’yan bindiga ba,” inji shi.

Kiran na Shugaban Kungiyar na zuwa ne a daidai lokacin da wata dattijuwa mai suna Aisha Muhammad take kokawa bisa garkuwa da ’yan sa-kai suka yi da danta Bafulatani a garin Sakkwato kusa da Giginya Sakatariya.

Malama Aisha ta shaida wa Aminiya cewa, dan nata mai suna Muhammad Bello magidanci ne da ke aikin gadi a wani gidan mai a yanki, kana idan garin Allah ya waye yana aikin debo ruwa ne ga masu buga bulo a yankin.

Ta ce kowa ya san shi a yankin, sama da shekara uku aikin da yake yi ke nan baya zuwa ko’ina.

“A ranar da lamarin zai auku da rana ne yana aikin debo ruwa tare da dansa suka iske shi suka sanya masa ankwa suka tafi da shi, yau sama da mako biyu ke nan, babu amo babu labarinsa.

“Kuma shi ke kula da ni mahaifiyarsa da kanwarsa da matarsa da ’ya’yansa yara kanana su biyar,” inji ta.