A daina yi wa ma’aikata ritaya lokacinsu bai yi ba – dan kasuwa Umar
An bayyana irin yadda gwanatin baya ta rika yi wa mutane ritaya dag aiki ba bisa wa’adinsu yayi ba da cewa rashin adalci ne da kuma son zuciya. Malam Umar Jibrin Usman, dan kasuwa mazaunin Kalaba Jihar Kurosriba ne ya bayyana haka a zantawarsa da Aminiya. Ya ce tun daga lokacin da aka kafa mulkin […]
An bayyana irin yadda gwanatin baya ta rika yi wa mutane ritaya dag aiki ba bisa wa’adinsu yayi ba da cewa rashin adalci ne da kuma son zuciya.
Malam Umar Jibrin Usman, dan kasuwa mazaunin Kalaba Jihar Kurosriba ne ya bayyana haka a zantawarsa da Aminiya. Ya ce tun daga lokacin da aka kafa mulkin demokradiyya a kasar nan ta girku 1999 zuwa 2007, gwamnatocin baya sun ci karensu babu babbaka wajen fifita bangarensu da kuma kabilarsu, kana kuma da cin zarafin wata ba kaidi.Ya ce gwamnatin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ta zo, awon fari ’yan Arewa masu rike da manyan mukaman gwamnati da na tsaro ya fara yi wa ritaya. Sai da ya tabbata ya kasara Arewa sannan ya hakura. Na baya bayan nan kafin zuwan Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi wa kwamandan jami’an tsaro na Sibildifens, Alhaji Ado Ahmed Darki ritaya ba tare da lokacinsa ya yi ba.
Dangane da haka, dan kasuwar ya bukaci Gwamnatin Muhammadu Buhari ta sanya a binciki waccan ritaya da aka yi wa Ado Darki domin haka ya nuna ana fifita wani bangare kan wani, wanda hakan bai dace ba.
A waje daya kuma wakilinmu ya tuntubi Alhaji Ado Ahmad Darki wanda aka yi wa ritaya sai ya ce, “ai bakin alkalami ya riga ya bushe. Shekara biyu ke nan da yin ritayar, har ma ina karbar kudin fansho. Na gode wa duk mutanen da suka nuna damuwa da halin da aka shiga, musamman Umar Jibrin da ma sauran jama’a. Ina fata su taimake ni da addu’a, Allah Ya yi mani zabi da kuma sauyi na alheri”