A dakatar da shugaban makarantar da aka kai wa masu hijabi hari —MURIC
MURIC ta bukaci ta rufe makarantar domin hana tashin fitina
Shugaban Kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola
Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) ta bukaci a dakatar da Shugaban Makarantar Baptist High School, tare da rufe makarantar a sakamakon harin da aka kai wa dalibai masu sanya hijabi.
MURIC ta yi kiran ne bayan harin da ’yan daba da jami’an tsaro suka kai wa dalibai mata Musulmi a makarantar a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar lumana ta neman ’yancinsu na sanya hijabi a ranar Alhamis.
MURIC ta kuma yi kira da a rufe makarantar da ke yankin Ijagbo na Karamar Hukumar Oyun ta Jihar Kwara, domin dakile tashin fitina, bayan harin ya yi sanadiyyar jikkata mutum hudu, har kaa kwantar da dayansu a asibiti.
Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa ya kamata a dakatar da shugaban makarantar ba tare da bata lokaci ba.
Ya ce, “Duk da cewa ana rade-radin cewa an kashe mutum daya, ba za mu yi magana a kai ba, har sai mun samu cikakken bayani daga reshenmu na Jihar Kwara.
“Mun yi tir da harin kidahumanci da aka kai wa kananan ’yan mata da ke zanga-zangar lumana ba tare da daukar wani makami ko tayar da yamutsi ba.
“Zanga-zangar lumana halastacciyar hanya ce ta bayyana korafi ko nuna rashin jin gamsuwa da wani, buddin aka gudanar da zanga-zangar cikin lumana,” a cewar Farfesa Akintola.