‘A daki daya muke kwana da Sarkin Kano Sanusi’

Har yanzu muna nan kamar yadda muke a baya.

‘A daki daya muke kwana da Sarkin Kano Sanusi’

Sanusi tare da Nasiru Ado Bayero

Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, ya ce sun kasance aminan juna da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II tun tale-tale.

Ana iya tuna cewa, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya nada Sanusi wanda ke zaman tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, a matsayin Sarkin Kano na 14 bayan rasuwar marigayi Alhaji Ado Bayero.

Biyo bayan rarraba masarautar Kano gida hudu, Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tumbuke rawanin Sanusi a bara, kuma ya maye gurbinsa da babban yayan Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero.

A wata doguwar tattaunawa da Aminiya ta yi a yayin da ake shiryen-shiryen bikin mika masa sanda da kuma auren diyarsa, Sarkin Bichin ya ce akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da korarren Sarkin Kano wacce ana iya daukarta a yi dogon nazari a kanta.

“Tare muka taso, amma ya girme ni da kusan shekaru uku kuma mun kasance aminan juna tun fil azal.

Sarkin Bichin ya ce bayan Sanusi ya dawo fadar Sarkin Kano, a daki daya suka yi rayuwa tun daga kuruciya har suka girma.

“Tare muke karin kumallon safe kuma mun kasance shakikai don babu wasu masu kusanci a duk dangi da ya kai wanda yake tsakani na da shi.

“Aminantakar da ke tsakanina da shi ana iya yin nazari a kanta don ko mahaifanmu tare suka taso.

Dangane da ko an samu sauyi a alakar da ke tsakaninsu, Nasiru Ado ya ce har yanzu akwai kyakkyawar alaka a tsakaninsu kuma sukan tuntubi juna lokaci zuwa lokaci.

“Har yanzu muna nan kamar yadda muke a baya, babu wani sauyi da aka samu dangane da dangartaka ta da shi,” a cewar Sarkin Bichi.

Ku ci gaba da bibiyarmu domin samun cikakkiyar tattaunawar da Aminiya ta yi da Sarkin na Bichi.