A dambace tsakanin shugaban karamar hukuma da Shugaban Ma’aikata a Adamawa
An dambace a tsakanin wasu ’ya’yan Jam’iyyar APC inda suka rika kai wa juna naushi a gidan tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da ke Yola a Jihar Adamawa.Waxanda suka dambacen kamar yadda Aminiya ta samu bayani su ne Alhaji Abdulrahman Abba Jimeta Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Adamawa da Shugaban karamar Hukumar Yola ta Kudu […]
An dambace a tsakanin wasu ’ya’yan Jam’iyyar APC inda suka rika kai wa juna naushi a gidan tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da ke Yola a Jihar Adamawa.
Waxanda suka dambacen kamar yadda Aminiya ta samu bayani su ne Alhaji Abdulrahman Abba Jimeta Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Adamawa da Shugaban karamar Hukumar Yola ta Kudu Alhaji Salihu Baba Ahmed.
Aminiya ta gano cewa waxanan jami’ai biyu sun dambace ne a lokacin da Atiku Abubakar ke ganawa da Gwamna Umar Bindow da shugabannin kananan hukuman jihar 21 da wasu magoya bayansu kuma sun fara zantawa, sai Salihu Baba Ahmed ya iso, kuma isowarsa ke da wuya sai suka fara sabani, inda aka ce masa lallai ya fita domin ba a gayyace shi ba.
kin fita daga wurin ne ya haifar da faxa wa juna bakaken maganganu da suka haifar fara naushin juna na gaban Atiku da Gwamna Bindow.
Daga baya wasu jami’an tsaro sun shiga wurin inda suka fitar da Salihu daga gidan Atiku sannan aka ci gaba da ganawar da ake yi.
Daga baya Salihu Baba Ahmed ya fitar sanarwa ga manema labarai cewa ya dakatar da magoya bayan Bindow daga aiki saboda rashin kunya da rashin girmamawa da suke nuna masa.
Sai dai a martanin Abdulrahman Abba Jimeta kan sanarwar da Salihu ya yi ya ce ba zai yi faxa da Baba Ahmed ba.
Kakakin Jam’iyyar APC a Jihar Ahmed Lawal ya ce kada jama’a su damu da maganar da Salihu na cewa an dakatar da Abba Jimeta daga aiki ba. Kuma ya ce babu wata ganawa da aka yi a gidan tsohon Mataimakin Shugaban kasar wanda ba a gayyace su ba. Ya ce an tsige Salihu daga shugabancin karamar hukumar, amma an yi hakan ne kawai kan ra’ayi ba tare da sa hannun jam’iyyar ba.