A dauki karin jami’an tsaro a Najeriya
Samun Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa. Hakan wata babbar nasara da jin dadi ne ga yan’Najeriya. Hakan kuma bai rasa nasaba da irin kyawawan halayen Shugaba Muhammadu Buharin. Duba da yadda ya taba rike mukamai daban-daban. dimbin al’umma kuma sun yi Allah sam barka da yadda ya jagorance su a kujerun da ya zauna […]
Samun Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa. Hakan wata babbar nasara da jin dadi ne ga yan’Najeriya. Hakan kuma bai rasa nasaba da irin kyawawan halayen Shugaba Muhammadu Buharin. Duba da yadda ya taba rike mukamai daban-daban. dimbin al’umma kuma sun yi Allah sam barka da yadda ya jagorance su a kujerun da ya zauna akai. Sai bayan da dimbin al’umma suna yabawa da sam barka, sai kuma wasu gurbatattun shugabanni suka fara yun kurin wargaza kasar tamu, ta hanyar jefa kusan illahirin ’yan kasar cikin mummunan yanayi na kuncin rayuwa.
Al’umma da dama sun galabaita a hannun wadancan gurbatattun shugabannin.Wanda hakanne ya sa al’ummar suka tashi haikan wajen yin addu’o’i ba dare ba rana a Masallatai/Majami’u da sauran wurare da dama.Inda suke rokon Allah ya canza masu gwamnatin da mafi alheri. Dayake Allah maji roko ne yaji kukan bayin nasa ya kuma biya musu da bukatar su ta hanyar ba su Muhammadu Buhari a matsayin wanda zai jagorance su a kasar baki daya.
’Yan’Najeriya sun ga tasku da dama a zamanin gwamnatin da ta shude. Manyan bala’o’i da musifun da suka gani muraran babu kamar yadda ’yan ta’addar Boko-Haram suke yin rawar gaban hantsi ta hanyar zafafa kai hare-haren ta’addanci, musamman a wuraren da al’umma ke taruwa kamar Masallataida Majami’u da tashoshin mota da kasuwanni da gidajen holewa da na kallon kwallo. A wadannan wurare ’yan’Boko-Haram sun hallaka dimbin mutane a zamanin gwamnatin da ta gabata. Amma cikin ikon Allah hawan Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa ’yan ta’addar Boko-Haram suka fara tattara yanasu-yanasu suna arcewa daga Najeriyar don sanin inda dare ya yi musu. Domin sun san irin luguden wutar da Shugaba Buhari zai sa a yi musu. Sai dai sauran ’yan daidaiku da suka boye a cikin gidaje, tare da sauran al’umma marasa kishin kasa.
Sheke aya da Boko-Haram suka yi a wancan karin takai ta kawo har suna jan daga da Sojoji, tare da kwace wasu kananan hukumomi da dama, inda suka maida su a karkashin su suka kafa tutocin su. To, amma yanzu zaratan Sojojin Shugaba Buhari sun samu nasarar kwato duk wata karamar hukumar da ke a hannun su, inda kuma suka ranta a cikin na kare.
Tabbas! Gwamnatin Muhammadu Buhari ta taka matukar rawar gani wajen samar da zaman lafiya. Sai dai duk da haka,ina mai bai wa Buhari shawara, tunda har ya fara karya laggon ’yan ta’addar ya kamata yanzu ya maida hankali wajen daukar jami’an tsaro tun daga Sojojin sama da na ruwa da na kasa, har ma da karin wasu jami’an tsaron da suka hada daJakmi’an shige da fice da na Kwastam da na farin kaya da ’yan sanda da ’yan banga da duk wani kaki, wanda zai samar da zaman lafiya. Domin karancin Jami’an tsaron ne ya sa har ’yan ta’ddar da ke cikin mutanen gari suke ci gaba da kai hare-haren a wurare daban-daban. Idan har Gwamnatin Buhari ta dauki wadannan Jami’an tsaro tabbas za su iya toshe duk wata kafa da wasu miyagu ke shigowa.
Na san yadda ake da dimbin matasa zauna gari banza da suka kammala makarantu, amma babu aikin yi za a same su da dama masu sha’awar samar da tsaron. Ina ganin watakila wani zai ce ai kasar mu a yanzu ba ta da kudin da za ta dauki tarin yawan wadannan jami’an tsaro ba. Ko kuma yadda muke da tulin matasa masu neman aikin yi ido rufe, ko da misali ana bai wa Jami’in tsaro Naira dubu 50 a duk wata a ce ma matasan za a dauke su aikin samar da zaman lafiya, amma sakamakon karancin kudi da kasa ke fama da shi madadin a rika ba su dubu 50, su yi hakuri a rinka ba su dubu 30 ko 25 a duk wata, har zuwa lokacin da kasa ta kara warwarewa, t ayadda za samu abin biyan su albashin Naira dubu 50 din. Na yi imanin matasan mu za su yi na’am da hakan.
Kuma hakan zai sa duk inda wani dan ta’adda yake cikin gari ko daji za su iya zakuloshi. Sannan a kara yawan masu unguwanni domin su ma sun yi karanci ya kamata a ce mai unguwa daya gidajen da ke karkashinsa kada su wace 100. Idan har aka yi haka to ina tabbatar da cewa ko da bakuwar kaza ce aka yi mai unguwa zai gane ko ta wane gida ce. Sannan Mai unguwar ya kasance dan cikin unguwar ne. Haka suma jami’an tsaro.
Insha Allahu idan Gwamnatin Buhari ta yi amfani da wannan shawara tawa za a kawo karshen ’yan ta’adda a kasar mu. Domin duk yadda ake son a samar da ci gaba idan har babu zaman lafiya ci gaba ba ya samuwa. Da fatan wannan shawara tawa ta iso inda ya dace, a kuma yi nazari akan ta da kyau.
Haruna Muhammad Katsina, shi ne, Shugaban kungiyar Muryar Jama’a. 07039205659 ko 07057491050 [email protected]