‘A dauki nauyin karatun talakawa da alawus din ‘yan majalisar tarayya’
Shugaban matasan jamiyyar LP wato labour Party a Kuros Riba reshen unguwar hausawa, Alhaji Tijjani danhajiya ya ce yunkurin da ake yi na rage kudaden da ‘yan-majalisar kasa suke karba ya yi daidai. danhajiya ya ce ganin halin da kasarnan ta samin kanta a yanzu na rudani a bangaren tattalin arzikin dole ne ‘yan majalisa […]
Shugaban matasan jamiyyar LP wato labour Party a Kuros Riba reshen unguwar hausawa, Alhaji Tijjani danhajiya ya ce yunkurin da ake yi na rage kudaden da ‘yan-majalisar kasa suke karba ya yi daidai.
danhajiya ya ce ganin halin da kasarnan ta samin kanta a yanzu na rudani a bangaren tattalin arzikin dole ne ‘yan majalisa su hakura da wasu alawans-alawans da ake basu na ba-gaira ba-dalili.
Ya bada misalin cewa “ya kamata a rage kudin alawus na ‘yan majalisar kasa da suke gudanar da ayyukan mazabun su da ofisoshin su”.
Alhaji dan hajiya ya ce “ina ganin ya kamata a yi amfani da kudin wajen biyawa ‘ya ‘yan talakawa da marasa galihu dake karatu tun daga matakin firamare zuwa na jami’a, misalia jaha mai sanatoci uku mai makon a basu kudin gaba daya a duba ‘ya’ayan marasa galihu a biya masu kudin makaranta domin sama da shekara hudu idan ka je wata mazabar dan majalisar ba zaka iske an yi hanyar mota ko asibit da jama’a za su amfana ba wasun su ma kauracewa mazabun su sukeyi. Wasu daga cikin ‘yan majalisun kwanciyar su kawai sukeyi a Abuja basu ko lekawa mazabunsu bare ma su san da damuwar mutanen mazabar su”.