A dawo da shirin yaki da rashin da’a – Sarkin Tilde
Sarkin Tilden Fulani kuma Hakimin Gundumar Tilden Fulani da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Aliyu Muhammad Tukur ya yi kira zababben Shugaban kasa Muhammad Buhari ya dawo da shirin yaki da rashin da’a da gwamnatinsa ta kaddamar a lokacin da ya jagoranci kasar nan a zamanin mulkin soja. Sarkin ya yi wannan […]
Sarkin Tilden Fulani kuma Hakimin Gundumar Tilden Fulani da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Aliyu Muhammad Tukur ya yi kira zababben Shugaban kasa Muhammad Buhari ya dawo da shirin yaki da rashin da’a da gwamnatinsa ta kaddamar a lokacin da ya jagoranci kasar nan a zamanin mulkin soja.
Sarkin ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a fadarsa, inda ya ce wannan shiri yana da kyau domin lokacin da aka gudanar da shi kowa ya shiga hankalinsa.
“Babu shakka dawo da shirin zai magance irin yadda mutane suke mugun gudu da ababen hawa ba bisa ka’ida ba. Kuma jama’a za su kwashe sharar tare da tsabtace muhallinsu. Sannan za su rika shiga layi a asibitoci da bankuna da gidajen mai da sauransu. Don haka dawo da shirin zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da bin doka da oda a kasar nan,” inji shi.
Har ila yau Hakimin ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da hankali kan maganar inganta samar da wutar lantarki a kasar nan. Ya ce idan aka samu wutar lantarki
za a saui isassun masana’antu da miliyoyin matasa za su samu ayyukan yi.
Ya ce “Idan babu wutar lantarki masana’antu ba za su samu ba, don haka ya zama wajibi, a farfado da wutar lantarki a kasar nan.”
Hakimin ya bukaci Buhari ya mayar da hankali kan magance matsalolin rashin tsaro da cin hanci da rashawa da suke addabar al’ummar kasar nan. Ya ce al’ummar kasar nan sun sha wahala saboda lalacewar tsaro, don haka ya dace a duba wadannan matsaloli.
Daga nan ya yi kira ga al’ummar Najeriya su bai wa Shugaban kasar mai jiran gado goyon baya da hadin kai domin ya kai ga nasara wajen gudanar da mulkinsa.