A dora wa kananan hukumomi laifin tarzomar da ke aukuwa a yankunansu – Gogel
Wani jagoran al’umma a yankin Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Sani Idris Gogel ya yi Allah wadai da yawaitar aukuwar rigingimu a wasu yankunan kasar nan, inda ya zargi shugabannin kananan hukumomi da sakaci wajen tsawata wa jama’arsu. Alhaji Sani Idris wanda shi ne Uban kungiyar Masu Gidajen Wanka ta Abuja, ya ce akwai bukatar a […]

Wani jagoran al’umma a yankin Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Sani Idris Gogel ya yi Allah wadai da yawaitar aukuwar rigingimu a wasu yankunan kasar nan, inda ya zargi shugabannin kananan hukumomi da sakaci wajen tsawata wa jama’arsu.
Alhaji Sani Idris wanda shi ne Uban kungiyar Masu Gidajen Wanka ta Abuja, ya ce akwai bukatar a tilasta wa kananan hukumomi biyan diyyar asarar da jama’a suka yi a yankunansu duk lokacin da rikici ya auku, ta hanyar zabtare kudin asusunsu don ya zame musu darasi.
Alhaji Sani Gogel ya yi Allah wadai da kona Kasuwar Bwari da ake zargin wadansu matasan yankin da aikatawa, inda ya bukaci Ma’aikatar Birnin Tarayya ta tallafa wa wadanda matsalar ta rutsa da su kuma ta cika alkawarin da ta dauka na ladabtar da masu hannu a lamarin.
Alhaji Sani Gogel ya yaba wa Gwamnan Jihar Filato Mista Samuel Bako Lalong kan matakin da ya dauka na dakatar da wani shugaban karamar hukuma a jihar a kwanakin baya, sakamakon aukuwar tarzoma a yankinsa. “Idan gwamnoninmu suna daukar irin wannan mataki za a samu saukin fitintinu a wuraren da suka yi kaurin suna wajen aukuwar tashin hankali,” inji shi.