A duba batun mutuwar jarirai a wajen haihuwa

 A kwanakin baya wata likitar yara, Dokta Efunbo Dosekun ta bara, inda ta ce kusan jarirai 700 ne suke mutuwa kullum a yayin haihuwa a kasar nan. Ta ta’allaka faruwar haka ga rashin na’urorin kyankyasa a asibitocin kasar nan da sauran matsaloli. Kuma ta ce akwai karancin kwararrun ma’aikata da rashin ingantattun gine-ginen asibitoci da sauransu, […]

A duba batun mutuwar jarirai a wajen haihuwa
A duba batun mutuwar jarirai a wajen haihuwa

 A kwanakin baya wata likitar yara, Dokta Efunbo Dosekun ta bara, inda ta ce kusan jarirai 700 ne suke mutuwa kullum a yayin haihuwa a kasar nan. Ta ta’allaka faruwar haka ga rashin na’urorin kyankyasa a asibitocin kasar nan da sauran matsaloli. Kuma ta ce akwai karancin kwararrun ma’aikata da rashin ingantattun gine-ginen asibitoci da sauransu, wadanda suka taimaka wajen haddasa mace-macen jarirai a yayin haihuwa.

Dokta Dosekun ta ce tsarin harkar kiwon lafiya ba ta da inganci a Najeriya, musamman ta bangaren aikin ceton rai. Wani rahoto na Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya nuna cewa a kullum a Najeriya ana rasa rayukan yara ’yan kasa da shekara biyar kimanin 2,300 da kuma mata masu juna biyu 145 da suke rasuwa a yayin haihuwa. Wannan ne ya sanya Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashen duniya da ake samun mace-macen yara da mata a yayin haihuwa. Wannan yana faruwa ne a yayin da Gwamnatin Tarayya da na jihohin ke ikirarin suna kokari wajen hanawa ko rage matsalar, yayin da a wasu jihohin ma har suke bayar da magunguna kyauta ga mata da yara ’yan kasa da shekara biyar kyauta. Idan da lallai gwamnatocin na kokari kamar yada suke fada, lallai da yanzu matsalar ta ragu, alhali ba haka abin yake ba, kamar yadda rahotanni ke tabbatarwa.

Adadin jarirai da matan da ke mutuwa a yayin haihuwa sai kara hauhawa yake, don haka akwai inda matsalar take, don haka ya zama wajibi a yi bincike sosai domin gano inda matsalar take, matukar ana son dakile mace-macen yara da mata a yayin haihuwa. Ya dace a ce an samar da asibitoci na musamman domin kula da yara da mata masu juna biyu. Haka kuma ya dace a ce akwai wadatattun likitocin yara da za su rika kula da majinyata a kan lokaci. Amma irin yadda asibitocin ake samun karanci ko rashin na’urar tallafa wa jarirai, abin takaici ne. Hatta ma asibitocin da ke da irin wannan na’ura, sai ka iske akwai matsalar wutar lantarki; wanda haka ke nuna cewa lallai akwai matsala. Da akwai kula, akwai likitocin yara wadatattu da kuma na’urori, lallai da an samu raguwar mace-macen yara da mata a yayin haihuwa.

Baya ga rashin na’urar ma, akwai karancin kwararrun ma’aikatan da za su sarrafa na’urar. Irin yadda ake samun hauhawar yara da matan da ke mutuwa a yayin haihuwa, shi ya tabbatar da haka. Duk inda ka duba a kasar nan, za ka iske matsaloli a bangaren ma’aikatun lafiya da asibitoci da wuraren shan magani. Wasu wuraren za ka iske akwai ma’aikata da likitoci amma babu magani, wasu wuraren kuma ga maganin a wadace amma babu kwararru kuma wadatattun likitoci da jami’an asibiti. Wasu wurare, musamman ma karkara, mutane sai sun yi tafiya mai nisa kafin su cimma asibiti. A irin wannan yanayi, sai ka ga majinyaci ya galabaita ko ya rasa ransa ma kafin ya kai ga zuwa asibiti, saboda nisan hanya da sauransu.

Mafi yawan asibitocin karkara babu motocin daukar marasa lafiya, wasu kuma babu gadajen kwantar da majinyata. Wannan kuwa abin takaici ne, domin kuwa babu kasar da ta san ciwon kanta da za ta yi wa sashin lafiya rikon sakainar kashi haka. Nan fa gwamnatin kasar nan ta shigo da tsarin Inshorar Lafiya, wanda hakan abin a yaba ne, sai dai kuma anya ana samun ingancin aikin yadda ya dace? Shin hukumomin inshorar suna kulawa da aikinsu yadda ya kamata? Mafi yawan al’ummar karkara ba su cikin tsarin, wadanda kuma su ne suka fi bukatar kula ta fannin lafiya, don haka ya kamata a yi wani abu domin inganta tsarin.

Lallai ya kamata gwamnati ta yi da gaske wajen inganta harkokin lafiyar al’umma. Ya kamata a magance yawan yaje-yajen aikin da ma’aikatan lafiya ke yi a kasar nan. A mayar da hankali sosai wajen samar da ingantatttar ma’aikatar lafiya a sassan kasar nan, domin inganta harkar kula da lafiyar al’umma.