A duba dabarun tsaro 15 na Shema
Wannan shi ne ke damuna! Idan har Allah Ya amsa muku addu’o’inku saboda darajar wannan wata mai albarka, to ya kamata ku yi wani abin a-zo-a-gani daga cikin wannan rabauta da ya yi muku. Na fadi haka ne domin kuwa sai na ga cewa idan Allah Ya wadata ku daga ni’imominSa ko ya kara muku […]
Wannan shi ne ke damuna! Idan har Allah Ya amsa muku addu’o’inku saboda darajar wannan wata mai albarka, to ya kamata ku yi wani abin a-zo-a-gani daga cikin wannan rabauta da ya yi muku.
Na fadi haka ne domin kuwa sai na ga cewa idan Allah Ya wadata ku daga ni’imominSa ko ya kara muku kan dan abin da kuke da shi domin alfarmar wannan wata, to ya kamata ku dinga fitar da Zakka, wanda yawancinku ba sa yi. Shin kun manta cewa a cikina ne na ji a lokacin tafsir, malaminku da ke yin wa’azi na fadar ku dinga fitar da hakkin Allah daga dukiyoyin da Allah Ya ba ku?! A lokacin da ake wannan wa’azi a cikin watan na Ramadan, wallahi na dauka cewa wa’azin na shigarku, musamman da malamin ke fadar, dan kyas ne Ubangiji ke bukata daga tarin dukiyar da Ya ba ku, kuma in kun mayar maSa, zai ninnika muku. Na ga wannan ai ita ce garabasa, amma me kuka yi bayan nan?
Ba kwa komai sai rashin hus! Da kun kwashi taku awalajar da rabaucin Allah shi ke nan, bayan watan Ramadan ya wuce, kun mance alkawarin da kuka dauka wajen Allah na fitar da Zakka da yin sadaka. Ba ku kara tunawa da Allah kuma sai wani watan Ramadan ya kama! Wannan ba sai na sake jaddada muku ba, wallahi ba daidai ba ne, amma ku sani ni na fita hakkinku a matsayina na Masallaci, domin na fadakar da ku kan abin da kila kun manta ko kuma kuna yi cikin ganganci! Ni dai ko a ranar tashin kiyama na san hanyarmu ba za ta kasance daya ba, sai dai kafin lokacin ku tuna da irin abin nan da Hausawa ke cewa, idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira!
Batu na karshe da nake so na amaye muku a yanzu daga nazarin da na yi muku a lokacin da kuke cikina kuna bauta a cikin wannan wata mai alfarma, ba ni ne abin ya fi damu ba, a’a, Yayana ne na ji yana korafi kan shi, wato Masallacin Idi! Wata rana ne muna tattaunawa a lokacin da muke taron zuri’ar gidanmu, ya ce ni da nake ta surutu kan masallatan da ke zuwa cikina salloli biyar da nafilfilin dare da i’itikaf, ai ban ga komai ba game da halayen ’yan Adam! Wannan abu ya ba ni mamaki! Amma duk da haka na kasa kunne don in ji inda kuke bata wa babban Yaya. Ya ce da ni, (duk kuwa da ba cewa ya yi na bayyana muku ba), ba inda kuke ba shi haushi sai ranar Sallar Idi ko bayan an sauko daga Sallar Idin, wato bayan an kammala azumin watan Ramadan. Ya ce da alama tun kafin watan azumin da kuma cikin watan kuke shirin saba wa Maiduka daga irin shirye-shiryen da kuke yi. Ya ce, yadda kuke zabar kayan da za ku sa domin halarta harabarsa ya kara tabbatar masa cewa ba don Allah kuke yin abin da kuke yi ba! Wallahi har rantsuwa ya yi da Allah zai ba shi izini da wasu daga cikinku ba ku yi Sallah a cikinsa ba! Ya ce da sai ya yi bore da atire idan kuka tako cikin harabarsa. Matsalar kamar yadda na fahimta ita ce yadda kuke zabar tufafin da za ku dinka; na yarda Allah Ya amince ku ci kwalliya a wannan rana ta zuwa harabar su Yaya Masallacin Idi da kuma cin kwalliyar bayan Sallar Idin, amma wace irin kwalliya ce ya ce ku yi? Ku shiga kasuwa ku saya wa ’ya’yanku tufafin da ba za su rufe tsiraici ba? Ko ku shiga kasuwa (musamman mata) ku sawo yadin shadda ko leshi ko atamfa wadanda ba wadatattu ba, ku ce wa tela ya dinka wa ’ya’yanku fited, su shiga gari yawon Sallah tamkar suna zindir? Ko kuma ka ga ’yan mata sanye da hijabi tutur zuwa wurin su Yaya Masallacin Idi, bayan Sallar Idin kuma ka nemi hijabin sama ko kasa. Uhum, na ji ma kuna kiran hijabin naku da wani abu wai shi wizi, alhali ba sunansa ke nan ba, sai dai tsiraici!
Kamar yadda Yaya Masallacin Idi ya bayyana mani, a duk lokacin da kuka ratsa harabarsa za ku yawon Sallah ji yake tamkar ya kame kafafunku, ya hana ku motsawa! Domin Allah ba cewa Ya yi ku yi yawo a doron kasa tsirara ba!
Kai abin da yawa, sai dai a yi man tsahiri sai wani karon, domin kuwa Magajina Masallacin Juma’a shi ma ya kawo kokensa, amma da yake ba huruminsa ba ne, na sa a mala!
Daga karshe ina yi muku fatar alheri a cikin wannan wata mai alfarma da ya sake zagayowa! Allah Ya sa ku ci karo da Lailatul kadari. Allah Ya sa duk abin da kuke bata dare kuna roko a wannan watan, ya zama amsasshe daga Maiduka. Allah Ya sa duk abubuwan alherin da kuke yi a cikin watan Ramadan ku ninka, ninkin-ba-ninkin bayan watan Ramadan!
Ku tuna duk lokacin da kuka ji Ladan na kiran Sallah zuwa gare ni, sako ne yake isarwa zuwa gare ku. Shin in ya ce Allah Akbar! Kun kuwa yarda cewa Allahn ne Mafi girma? Idan ya ce Asshadu Alla’ilaha illalah, shin kun kuwa amince cewa babu wanda ya cancanci bauta sai Allah? Idan ya ce da ku Asshahadu anna Muhammadar Rasulullah, shin a cikin ranku, kun aminta lallai Annabi Muhammad Manzon Allah ne?! A lokacin da yake ce da ku, Hayya alas Salah, kuna kuwa hanzartawa cikin gaggawa? In ya ce da ku Hayya alal falah, shin kuna famfalakawa zuwa ga wannan babban rabo? Ku sani duk wanda ya yi abin da Allah bai amince da shi ba, to bai amsa kiran Ladan ba ke nan, Sallar dai ake yi! Na gode!’
Naku, dan uwanku, Masallaci!