A duba matsalolin malaman makaranta

A makon jiya ne malaman makaranta a Najeriya suka bi sahun ’yan uwansu na duniya wajen bikin Ranar Malamai ta Duniya, inda a nan kasar malaman na makaranta suka yi jawabai wajen sake kwarmata matsalolinsu da nufin neman a magance su. A yayin da yake taya malaman murnar wannan rana, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya […]

A duba matsalolin malaman makaranta
A duba matsalolin malaman makaranta

A makon jiya ne malaman makaranta a Najeriya suka bi sahun ’yan uwansu na duniya wajen bikin Ranar Malamai ta Duniya, inda a nan kasar malaman na makaranta suka yi jawabai wajen sake kwarmata matsalolinsu da nufin neman a magance su.

A yayin da yake taya malaman murnar wannan rana, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira da a samu sauya hali da yanayi daga malaman makaranta. Ya ce hakan ya zama wajibi, domin a samu fa’ida ga kudurin gwamnati na gyara al’amuran ilimi, musamman ma bunkasa harkar koyo da koyarwa a kasar nan. Jawabin Shugaban kasar ya fito ne daga bakin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Injiniya Babachir Lawal, a yayin gangamin da malaman makaranta suka shirya a Abuja.
Shugaban kungiyar Malamai ta kasa (NUT), Michael Olukoya, ya yi amfani da wannan biki wajen kira ga Shugaban kasa da ya duba matsalolin da ke ci wa harkar ilimi tuwo a kwarya a kasar nan, musamman ma matsalolin da suka addabi malaman makaranta. Ya bayyana cewa, an kashe sama da malaman makaranta 600 a yankin Gabashin-Arewa a cikin shekaru shida da suka gabata, a sakamakon rikicin Boko Haram. Ya kuma ce malamai 19, 000 suka samu kansu a matsayin ’yan gudun hijira a sakamakon wannan ta’addanci don haka ya yi kira ga gwamnatocin kowane matakai su tsaurara tsaro ga makarantu na ko’ina.
Shi kuwa shugaban kungiyar na Jihar Kwara, Kwamared Musa Abubakar, ya tabbatar da cewa a shirye suke su nuna tirjiya da kin amince wa duk wani yunkurin mayar da alhakin kula da ilimin firamare ga kananan hukumomi. Maimakon haka, ya ba da shawarar da a kirkiro hukumar da za ta kula da al’amuran makarantun sakandare da ke karkashin Gwamnatin Tarayya.
Mu kuwa a ganinmu, wadannan bukatu biyu na Kwamared Musa Abubakar, dukkansu suna da matsala. Na daya, hakkin kula da ilimin firamare, hakki ne da ya rataya ga wuyan kananan hukumomi, kamar yadda tsarin mulki ya tanada. Da ya yi kira da a kafa hukumar kula da makarantun sakandare mallakar Gwamnatin Tarayya kuwa, ya kamata ya yi la’akari da cewa ai makarantun sakandare mallakar jihohi sun fi yawa, kasancewar ita Gwamnatin Tarayya makarantun sakandare guda 109 kacal ta mallaka. Haka kuma, tuni ake kukan cewa hukumomi da ma’aikatu sun riga sun yi wa Gwamnatin Tarayya yawa, domin hatta Kwamitin Oronsaye ya ba da shawarar a rage su, a hade wasu wuri guda.
Wata babbar matsala da ta addabi malaman makaranta, ita ce ta rashin biyan su hakkokinsu a kan kari. A yayin da yake jawabinsa a wurin bikin Ranar Malaman Makaranta ta Duniya, Kwamared Olukoya ya bayyana cewa, rashin biyan malamai hakkokinsu a kan kari, rashin tausayi ne kuma babban laifi ne. A wasu jihohin, ana biyan malaman makaranta kashi 50 ne kawai cikin dari na albashinsu. A wasu jihohin kuwa, suna bin bashin albashin watanni ne, a yayin da ba a biyan su kudin hutu da sauran alawus-alawus masu yawa.
Mafi yawan matsaloli da kalubalen da malaman makaranta ke fuskanta a yau, a can baya ba a san su ba, musamman ma lokacin da Shugaba Ibrahim Babangida ya kirkiro Hukumar Kula Da Ilimin Firamare ta kasa (NPEC). A lokacin nan ba a san wani abu asusun hadin gwiwa tsakanin jihohi da kananan hukumomi ba. A lokacin nan, dukkan hakkokin malamai, ana cire su ne kai tsaye zuwa asusun hukumar NPEC, don haka babu wata hanya da ake bi wajen wawure kudinsu a matakin wata jiha ko karamar hukuma. Ta haka kudaden malaman kai kai gare su kai tsaye daga hukumarsu zuwa hukumar ilimi ta karamar hukuma.
Matasala ta faro ne tun daga lokacin da aka kashe wannan tsari na baya, inda matsalar ta kara ta’azzara da aka kirkiro hukumar UBEC, inda nan ne aka samu tsarin asusun hadin gwiwa tsakanin jihohi da kananan hukumomi. Ta wannan hanya ce jihohi suka rika zare kudaden kananan hukumomi, har ma tare da na malaman makaranta. Domin ganin an magance matsalar nan, ya kamata gwamnati ta yi tunanin dawo da hukumar NPEC, a jingine UBEC.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50