A dubi ‘yan Najeriya da ke tsare a kasashen waje
Kiyasi ya nuna akwai ’yan Najeriya sama da dubu 15 a gidajen kaso na kasashen duniya wadanda ake tuhumarsu da laifuffuka daban- daban da suka hada da fataucin miyagun kwayoyi da safarar mata da kananan yara da ketare iyakoki ba bisa ka’ida ba da ayyukan ta’addanci da sace-sace da zamba cikin aminci da sauran laifuffukan […]
Kiyasi ya nuna akwai ’yan Najeriya sama da dubu 15 a gidajen kaso na kasashen duniya wadanda ake tuhumarsu da laifuffuka daban- daban da suka hada da fataucin miyagun kwayoyi da safarar mata da kananan yara da ketare iyakoki ba bisa ka’ida ba da ayyukan ta’addanci da sace-sace da zamba cikin aminci da sauran laifuffukan da suka saba dokokin kasashen duniya.
Yawan ’yan Najeriya da ke shiga komar jami’an tsaron kasashen waje yakan zarta na sauran kasashen Afirka, wannan ba ya rasa nasaba da yawan jama’ar da kasar nan ke da shi da kuma irin rikon sakainar kashi da wadansu ’yan kasar ke wa doka da oda a cikin gida da kuma waje.
Duk da irin laifuffukan da ’yan Najeriya ke aikatawa a kasashen waje, akwai wadanda akan shiga hakkinsu, ake cin zarafinsu ba tare da sun aikata wani laifi ba, akwai wadanda suke taka sawun barawo a kama su da laifin da ba su ji ba ba su gani ba. Akwai da yawa da ake sanya wa kayan laifi a halin tafiya ko a yi amfani da sunayensu da fasfo dinsu ko jakunkunansu da nufin aikata laifi yadda su masu shirya hakan in ta kwabe sai su zame su bar ’yan ba-ruwana da jidali. Wannan yana faruwa matuka kuma hukumomin kasashen ketare ba ruwansu da bincike kwakwara da nufin warware zare da abawa. Gwamnatin Najeriya ce kadai za ta iya yin wani abu domin tsamo su daga cikin mummunan halin karbar hukunci bisa laifin da ba su ne suka aikata ba. Babban misali a nan, shi ne yadda ya faru da wata budurwa Zainab Aliyu daliba a Jami’ar Maitama Sule da ke Kano wacce aka sanya wa miyagun kwayoyi cikin kayanta a kan haryarta ta zuwa aikin Umara a kasar Saudiyya, lamarin da ya jawo mata wahala musamman ganin yadda hukumomin Saudiyya suka yi kokarin zartar mata da hukuncin laifin da ba ita ta aikata ba.
Bisa addu’o’i da kuma sanya bakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta hannun Ministan Shari’a Allah Ya kubutar da ita. Ina so in yi amfani da wannan dama in jawo hankalin Gwamnatin Najeriya cewa irin wadannan matsalolin suna shafar jama’a da dama ’yan ba-ruwana ba Zainab Aliyu ba ce kadai ta shiga irin wannan taskun akwai da dama da a yanzu haka suke cikin wannan tasku.
’Yan Najeriya da dama suna gidajen yarin kasashen duniya daban-daban wadanda in har aka bincika ba su da laifin komai. Kwanakin baya na karanta wata budaddiyar wasika zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari wacce wadansu ’yan kasuwa a Kano suka rubuta don jawo hankalin gwamnati kan wadansu ’yan uwansu ’yan kasuwa wadanda suke harkar kasuwanci a Dubai da Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta tsare tsawon lokaci ba tare da laifinsu ba.
A kokarin yin tsokaci game da irin yadda wadansu ke fama da wahalhalu na ragaita a gidajen kaso na kasashen waje, na yi kokarin jin ta bakin ’yan uwan Ibrahim Ali Alhassan da Bashir Ali wadanda hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa suka tsare tsawon shekaru. A gaskiyar magana akwai bukatar bibiyar lamarin wadannan bayin Allah, musamman ganin yadda ake ta wasa da hankali game da abin.
Babban abin da ya kamata hukumomin Najeriya su yi shi ne bin diddigin duk wani dan kasar nan da ya shiga irin wannan hali don kuwa akwai da dama da ake sanya musu mugun kaya ba tare da saninsu ba kuma rashin tsayawa da bincike ke jefa mutane da dama cikin masifa, babban misali da ya fito fili shi ne rigimar da aka jefa Zainab Aliyua ciki.
A karshe ina kira ga dukkan hukumomin da wadannan al’amura suka shafa, kama daga Ma’aikatar Harkokin Waje da Ofishin Jakadancin Najeriya a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya da kuma kungiyoyin kare hakkin bil Adama na duniya, cewa allai ya kamata a duba wadannan bayin Allah, Ibrahim Ali Alhassan da Bashir Ali da sauran ’yan Najeriya da ake tuhuma da laifufuka daban-dabam a kasashen duniya don ganin an tabbatar da adalci a tsakaninsu.
Mudassir Aliyu Yunusa,
Imel; [email protected]