A fara mana shirin RUGA a jihohin da suka amince
Akwai jihohi 12 da suka ce sun aminta a fara aiwatar da shirin RUGA a jihohinsu, don haka nake ganin in har Shugaba Buhari da gaske yake son aiwatar da wannan shiri na matsugunnin makiyaya da ya yiwa lakabi da RUGA wato (Rural Grazing Areas) a kasar nan, to, sai ya fara daga wadancan jihohi […]
Akwai jihohi 12 da suka ce sun aminta a fara aiwatar da shirin RUGA a jihohinsu, don haka nake ganin in har Shugaba Buhari da gaske yake son aiwatar da wannan shiri na matsugunnin makiyaya da ya yiwa lakabi da RUGA wato (Rural Grazing Areas) a kasar nan, to, sai ya fara daga wadancan jihohi da gwamnoninsu suka yarda a yi musu. Wadancan kuwa da suka ki to, sai a kyale su dama tun farko an ce sai wadanda suke so ne za a yi a wurarensu. Kuma ina ganin ba komai ya hana sauran jihohi yarda da wannan shiri ba musamman na Kudu sai don suna adawa da ci gaban Arewarmu sauran jihohin Arewa kuwa da suka ki yarda da shirin sun ki yarda ne saboda adawa da gwamanatin Shugaba Buhari da kuma bambancin siyasa da ke tsakaninsu da Shugaban Kasa amma ba wai don shirin ba ya da amfani ga kasar nan ba.
Sannan ina so in yi amfani da wannan dama wajen bai wa Shugaba Buhari shawara, ina so Shugaba Buhari ya sani janye shirin RUGA da ya ce an yi to, ba komai zai kara wa masu adawa da shi ba illa kwarin gwiwa da jin cewa su suka hana a aiwatar da wannan shiri za kuma su ci gaba ne da yin katsalanda ga duk abin da suka ga zai yi wa kasar nan na alheri musamman ma Arewa tun da dama su ba kaunar Arewar suke yi ba. Yana da kyau Shugaba Buhari ya tuna wannan shi ne shiri na uku da ya kawo don magance matsalar da ke faruwa a tsakanin manoma da makiyaya, don haka bai ma kamata ya janye wannan shiri nasa na alheri da ya yi niyyar yi ba saboda wadancan marasa son ci gaban, tunda daman tun farko an ce sai jihohin da suke so ne za a yi wa. Don haka ina ganin da kamata ya yi ya ce da su za a aiwatar amma ban da jihohinsu tunda ba su so.
Bayan haka ina so ya sani in har da gaske yake son aiwatar mana da shirin RUGA sai ya tuna da cewa babu wani aiki na alheri da mutum zai yi niyyar yinsa face ya samu suka daga wadansu mutane musamman ma shi da yake Shugaban Kasa kuma dan kabilar Fulani wadanda ake ganin kamar su kadai shirin zai amfana. Kowa ya san wannan shiri zai taimaka wajen kawo karshen rigingimun da aka dade ana fama da su a tsakanin manoma da makiyaya a kasar nan. Duk dai da yake dama yawancin fadan ana fakewa da shi ne wajen cimma wata manufa ta siyasa, hakan ya sa ake ta adawa da duk wani shiri da zai tallafa wajen maganin wancan rikici da ke tsakanin manoma da makiyaya. Tambayata ana a nan ita ce;
1) Wai wadannan mutane da suka ce ba za a yi wannan shiri ba a jihohinsu wacce gudunmawa ko shawara suka kawo don magance fadan da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya?
2) Abin ba ya shafar su ne ko kuwa ba sa morar gudunmawar da Fulani suke bai wa kasar nan ne wajen samar da nama da (fatu) kiraga?
3) Me ya kawo Wole Soyinka cikin wannan maganar shi da ba Gwamna ba, ko kuwa an nemi shawararsa ce?
To, da wannan tambayar zan rufe wannan makalar tawa, kuma a karshe ina so Shugaba Buhari ya san cewa abin aljihu na mai riga ne, kuma ramin kura sai ’ya’yanta, don haka muke kira gare shi in har da gaske yake to ya fara aiwatar mana a jihohin da suka aminta. Allah Ubangiji Ya taimaki Arewa da ’yan Arewa da duk masu son ci gabanta Ya kuma ruguza duk wani da ke kinmu da yankinmu ko a birnin Makka yake.
Bello Kiyawa
Email:[email protected], 070-3252-8895