… A Faransa ana neman izinin shan taba a makarantu

Saboda dokar tabaci da Faransa ta kakaba a birnin Paris cikin Nuwamnbar bara, bayan an kai mata harin ta’addanci, malaman makaranta na ganin idan aka rika tura matasa wace su zuki taba, za su iya haduwa da hadarin ta’addanci.Kimanin kashi 32 cikin 100 na matasan Faransa, wadanda shekrun su ba su wuce 17 ba, sun […]

… A Faransa ana neman izinin shan taba a makarantu
… A Faransa ana neman izinin shan taba a makarantu

Saboda dokar tabaci da Faransa ta kakaba a birnin Paris cikin Nuwamnbar bara, bayan an kai mata harin ta’addanci, malaman makaranta na ganin idan aka rika tura matasa wace su zuki taba, za su iya haduwa da hadarin ta’addanci.
Kimanin kashi 32 cikin 100 na matasan Faransa, wadanda shekrun su ba su wuce 17 ba, sun tabbatar da cewa, suna zukarar karan taba a kowace rana, amma dokar kasa ta hana su shan tabar a cikin makaranta, don haka suke fita waje su sha kayan su. Su kuwa malaman makarantun da suka fahimci haka, suna ganin akwai yiowuwar akai wa yaran harin ta’addanci, kamar yadda kungiyar malaman makaranta ta kasa, mai lakabin SNPDEN-Unsa.
kungiyar SNPDEN-Unsa ta rubuta wa Firayiministan kasar, Manuel balls, inda ta bukaci a tantance matsayin dokar hana shan taba a cikin makaranta. Shin ko dokar tabacin har yanzu tana aiki, musamman ganin yadda ma’aikatar lafiya ta doge a kai? Ko kuma in an yi la’
Akari da hadarin rsahin tsaro da ka iya auka wa wadanda suka fito waje, shin shugabannin makarantu na iya yanke hukucin cewa, ban da su, tunda ma’aikatar ilimi na nuna alamun amincewa ko bayar da izinin shan taba a cikin makaranta? Wannan dai shi ne abin da ake ta ce-ce ku ce akai, musamman ma ganin cewa hadarin da ke tattare da harin bama-bamai ko harbin hbindiga bai kai na tabna ba.
“A zaba tsakanin taba sigari da illar da ke tattare da bindigar  Kalashnikob, tabbas hadarin su ba daya ba ne,” a cewar Michel Richard, wani shugaban makaranta a wannan kungiya ta malamai.
Babu ma wanda ke tunanin hana matasan Faransa zukar taba sigari kwata-kwata. Al’adar shan taba ta zama ruwan dare, domin a kawai kebabbun wurare na musamman da Faransawa ke shan taba. Kusan kowace shekara ana zubar da burbushin taba da ta kai ton 350, wadda nauyinta ya kai nauyin hamshakin kifin rowan nan na Whales guda biyu; kwatankwacin bburbushin tabar da ake sharewa daga titunan birnin Paris kadai ken an. Mafi yawan biranen kasashen Turai sun shawo kan bankar hayakin taba a shekaru 10 da suka wuce, ta hanyaar kakaba dim,bin haraji da fadakarwar illata lafiya da taba ke yi wa mashayanta, tare da tsauraran dokoki.. Adadin mutanen da ke shan taba ya ragu a Birtaniya da kashi 20 cikin 100; 13 zuwa 13 cikin 100 a kasar Norway, sannan da kashi takwas cikin 100 a daukacin kasashe masu arziki na OECD. Sai dai a kasar Faransa har yanzu adadin na nan inbda yake, domin kimanin kasha 25 cikin 100 na matasa ke shan taba a shekarar 2008, kai har ma sun karu. Taba ce kan gaba a jerin cuutttukan da ake iya maganin su, amma tana halaka mutane.
Gwamnatocin Faransa da dama sun yi matukar kokari, wajen hana shan taba, amma al’amarin ya ci tura.Kodayake a bara ba a kakaba haraji a kan taba ba.