A farfado da al’adar karance-karance

Al’adar karance-karance ta shafi wanda yake karantun, malamansa wadanda da dama daga cikin su kan yi rubutu wasu ma a kiraye su marubuta, da marubutan da ba malaman makaranta ba ne, sannan iyaye na taka rawar gani sai uwa uba gwamnati. Duk da dimbun matsalolin da suka addabe Najeriya ba wanda ya yi kamari kamar […]

A farfado da al’adar karance-karance
A farfado da al’adar karance-karance

Al’adar karance-karance ta shafi wanda yake karantun, malamansa wadanda da dama daga cikin su kan yi rubutu wasu ma a kiraye su marubuta, da marubutan da ba malaman makaranta ba ne, sannan iyaye na taka rawar gani sai uwa uba gwamnati. Duk da dimbun matsalolin da suka addabe Najeriya ba wanda ya yi kamari kamar harkar ilimi, musamman idan aka yi maganar karatu ko wayewar kai domin duk suna da alaka da juna, kuma yara ‘yan firamare ne ma’aunin ci gaban karance-karance!
Akan fara koyon karatu da iyawa a lokacin kuruciya, wasu yaran tun suna shekara uku zuwa biyar. Akan haka masana halayyar dan adama sun tabbatar da idan ana son dawo da al’adar karance-karance dole sai an dora yara ‘yan firamare a kan saiti, musamman matsalar ta fi yawa a nan Arewa, idan aka kwatanta da Kudu, duk da damar da muke da ita muna rubutu da harshenmu!
Wata matsala a wannan zamanin ita ce ta kallon talabijin walau fim ko tauraron dan Adam! Musamman domin ta wata fuskar akwai karancin marubuta ko littattafai a kasuwa da gidaje da makarantu! idan ka kwatanta da yadda ake haihuwa sai a haifi yara 100 ba tare da an yi musu tanadin rubutattacen littafi daya ba a garinku ko jiharku!
Marubutan ba su karatu, sai ka tara marubuta 100 ba su karanta ‘Dare dubu da daya’ ba, sai ka, ba su san Gandoki ba, kuma ba su san wa ya rubuta ‘Tauraruwa Hamada’ ba. An koma kallo maimakon karatu, kuma ‘yan fim din nan ba abin da suka kware sai a satar fasaha, sun koya wa matasa rashin kunya, mace ta saki soyayyarta kafin aure, suna barikanci! An dauke su kamar tauraruwa mai wutsiya a Arewacin Nijeriya, shi yasa wasu suke sulalewa Kudancin kasar don su ida watsewa! Dadin dadawa duk da ‘yan fim din yau da ‘yan uwansu matasan marubutan da dama daga cikinsu suna da digiri da difloma ko shaidar karatun zamani sai ka iske masu shaidara karatun firamare ma’abuta wasan kwaikwayon da marubutan farko sun fi su hikima!
Iyaye ke dora ‘ya’ya akan turbar zaman rayuwa, a yayin da wasu iyaye na tsare ‘ya’yansu tare da ba su cikakkiyar kullawa, wasu kan bar yara na tallar abin da bai wuce 200 ba, kuma a haka za su karar da ranar suna yawo a titunnan garin, sannan wasu kan je kwallo a sa masu ido suna yawon banza.
Idan ka dauki gwamnati akwai damar da za a gina laburari a cikin gari makarantu da masu yawo ranakun kasuwa ko ranar Juma’a da Lahadi don a baza a karanta masu rajista ma su ara! Su kansu jam’i’o’i suna da damar buga littattafai cikin rahusa a madabi’ar jami’ar, amma sai ka  rasa me yake faruwa! Malaman jami’a ba su ba dalibai masu fita aikin fassara ko hikimar kirkirar sababbin littattafai
Marubutan ba su cika karanta wani abu ba, balle su karantar. Koyarwa da Turanci ba ita ba ce matsalar, amma kowa ya san ana koyawar da Turanci bayan kowa daga minsitan zuwa kwamishinan ilimin duk sun san yaran nan ba su jin Turanci, sai ka iske wadanda ba su kai matsayin su koyar ba, suna koyarwa, kuma an gaza daukar mataki! A haka ake girmama kwalaye bayan ba komai a kwakwalwar malaman balle daliban. Sai ka iske mai sakandare satifike a da ya fi mai digiri a yau, musamman a zamanin satar jarrabawa!
daliban jami’a a wasu kasashe kan sami horon bincike da nazarin samun mafita, akan haka koyaushe daliban na fafutukar samun sahihin sakamako. Amma a kasata Nijeriya wani abin takaici shi ne, sai ka iske daliban jami’a a gida sun share watanni ko jaridu ba su dubawa ko an koma makaranta! Balle littattafan fanonin da suke karantawa ko wadanda suka shafi rayuwar yau da gobe.
Gwamnati za ta iya dawo da shirye-shiryen karanta labaran wasu shahararrun littattafai a gidajen radiyo da talabijin, ta yadda za a rika yin tambayoyi kuma ana ba yaran kyaututuka, ko da iyayensu suka  fada masu akwai alamar iyayen da suka tsare, suka kiyaye kan gane amsoshin! Sannan hukumar za ta iya daukar nauyin harkar ilimin baki dayansa, idan da gaske take, ta yadda za a buga miliyoyin littattafai ba bada kyauta don a koyar da Turanci ko ba su tarbiyyar da aka ga ta dace. Domin harkar karatu hakki ne ga ma’aikatar ilimi, musamman ilimin farko na firamare, yayin da daga firamare ne ake samun barayin gwamnati, ‘yan ta’adda, karuwai, ‘yan daudu da masu madigo. Gara a lankwasa itaccen tun yana danye!
Ana bukatar gwamnati a ta rika tattaunawa da dalibai da malamai a bainar majalisar tarayya da ta jihohi don a san matsalolin da suka shafi karatu da al’adar karance-karance, ta yadda za a dawo da fahimtar cewa ba wai kwalaye bane ilimi, “A’a” aiki da karatu tare da cin riba, sannan a ga bambanci tsakanin wada ya yi ilimi da wadanda basu yi ba, kar mu rika kullun gara jiya duk da ilimin!
Marubuta kan zama kamar helikwafotocin da za su rika yawo lunguna suna yakar ‘yan ta’adda, bi ofisoshi don tsotse tawadar alkalamin da zai sace kudin gwamnati tare da samun nasara dora al’umma a kan hanya. Akan haka farfado da harkar daya yake da yaki da cin hanci da rashawa!
Kafin a dawo da al’adar karance-karance sai marubuta sun karkata alkalumansu, an fara rubutu akan bangarori da dama wadanda za su ja hankalin makaranta mabambanta! Zasu gamsar da kowane rukuni, watau yara da iyaye da dattijai da tsofaffi! Ba wai irin tsarin da kashi 99 cikin 100 na littattafan kasuwar Kano kan soyayya ne tsagwaransu! A shiga fagen bincike da tarihi da nishadi da wasanni da jarunta da ilimi da addinai da al’adu da zamani da fasaha da kimiyya da tarbiyya da tatsuniyoyi da makamatansu.
A fili yake cewa marubuta sune gwamnati, idan aka yi maganar karatu ko karance-karance, a haka za su iya dasa son gaskiya da tsoron Allah a zukatan makaranta, musamman idan aka sami alkalamin da ba ya karya! Ta hannun marubutan da za su sadaukar da neman suna ko kudi a gajeren zango, tare da samun mataimaka da za a yi kira ga kyawawan ayyuka da hanni ga munana da burin tsaftace al’umma.

Buhari Daure Muryar Talaka +2347035986444 [email protected]

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50