A farfado da makarantun Fulani makiyaya a Najeriya – Sa’idu Maikano

Shugaban Kungiyar Matasan Fulani Makiyaya ta Najeriya Alhaji Sa’idu Maikano, ya yi kira ga gwamnatocin kasar nan su farfado da makarantun Fulani makiyaya, domin su ci gaba da karantar da ’ya’yan Fulani makiyaya, kamar yadda suka faro a shekarun baya. Alhaji Sa’idu Maikano ya yi wannan kira ne, a lokacin da yake zantawa da jaridar […]

A farfado da makarantun Fulani makiyaya a Najeriya – Sa’idu Maikano

Shugaban Kungiyar Matasan Fulani Makiyaya ta Najeriya Alhaji Sa’idu Maikano, ya yi kira ga gwamnatocin kasar nan su farfado da makarantun Fulani makiyaya, domin su ci gaba da karantar da ’ya’yan Fulani makiyaya, kamar yadda suka faro a shekarun baya.

Alhaji Sa’idu Maikano ya yi wannan kira ne, a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya, inda ya ce yanzu wadannan makarantun Fulani makiyaya sun mutu a sassan kasar nan, sabanin yadda aka bude su a baya.

Ya ce a wasu wuraren ma an hada wadannan makarantu da sauran makarantun gwamnati.

Ya ce farfado da  makarantu  zai taimaka wa  Fulani makiyaya, wajen ba su damar yin karatun boko da na addini.

Har’ila yau ya yi kira ga gwamnatocin kasar nan, su fara biyan ardo-ardon Fulani alawus, saboda irin ayyukan da suke yi na jagorancin al’ummominsu.