A farfado da tattalin arzikin ’yan kasuwar Arewa – Kega

Shugaban Kungiyar Dillalan Motoci ta Najeriya Reshen Jihar Filato, kuma Shugaban Kamfanin Sayar da Motoci na Kega Motors da ke Jos a Jihar Filato, Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohin Arewa su hada kai su sake farfado da tattalin arzikin ’yan kasuwar Arewa. Alhaji Yahaya Muhammad […]

A farfado da tattalin arzikin ’yan kasuwar Arewa – Kega

Alhaji Yahaya Muhammad Kega

Shugaban Kungiyar Dillalan Motoci ta Najeriya Reshen Jihar Filato, kuma Shugaban Kamfanin Sayar da Motoci na Kega Motors da ke Jos a Jihar Filato, Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohin Arewa su hada kai su sake farfado da tattalin arzikin ’yan kasuwar Arewa. Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a garin Jos, inda ya ce ’yan kasuwar kasar nan, musamman na Arewa sun shida cikin wani mawuyacin hali cikin shekara hudun da suka gabata, kuma ba a yi musu wani abin a zo a gani ba ta fannin ci gaban harkokin kasuwancinsu.

Ya ce babban ci gaban da ’yan kasuwar suka samu shi ne zaman lafiya, amma maganar tattalin arzikin ’yan kasuwa sai dai a yi shiru kawai.

“Don haka muna fata a wannan karon abubuwa za su canja, a dubi matsalolin matsi da kuncin da ’yan kasuwa suke ciki, musamman a nan Arewa. Domin a Arewar ce ’yan kasuwa suka fi shan wahala. Amma wasu yankunan kasar nan, duk da kukan wahalar da ake yi, harkokin kasuwancinsu suna tafiya yadda suka kamata. A sake bude kamfanonin Arewa, domin mutane su samu aikin yi. Kasuwanci ya bunkasa, haka zai sanya harkokin tattalin arzikin talakawa su farfado,” inji Kega.