…A Filato ma an fara tantance maniyyatan jihar
A shirye-shiryen da Hukumar Alhazai ta Jihar Filato ke yi don gudanar aikin Hajjin bana hukumar ta fara tantance maniyyatan da za su tafi aikin Hajji daga jihar.Da yake zantawa da ’yan jarida a Jos Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Alhaji Salisu Musa ya ce sun fara tantance maniyyatan jihar ne saboda su tabbatar maniyyatan […]
A shirye-shiryen da Hukumar Alhazai ta Jihar Filato ke yi don gudanar aikin Hajjin bana hukumar ta fara tantance maniyyatan da za su tafi aikin Hajji daga jihar.
Da yake zantawa da ’yan jarida a Jos Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Alhaji Salisu Musa ya ce sun fara tantance maniyyatan jihar ne saboda su tabbatar maniyyatan sun san yadda ake aikin Hajji. “Muna son dukkan maniyyatanmu su san abin da za su yi, idan sun isa kasa Mai tsarki, ba za mu bar maniyyacin da bai san abin da zai je yi ba, ya tafi aikin Hajji,” inji shi.
Alhaji Salisu Musa ya ce tuni sun samar wa maniyyatansu masaukai masu kyau a Makka da Madina, kuma sun kammala dukkan shiryen aikin Hajjin bana, abin da ya rage musu shi ne bizar alhazansu.
Ya ce a bana maniyyata 1, 274 ne daga jihar za su sauke farali, inda ya yi kira su kasance masu bin doka da oda tun daga nan gida Najeriya zuwa Saudiyya.